Na gwamna masu gida rana –Tattalin arziki da harkokin ciniki a duniyarmu ta yau | Learning by Ear | DW | 18.01.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Learning by Ear

Na gwamna masu gida rana –Tattalin arziki da harkokin ciniki a duniyarmu ta yau

A'a, ba gano wata dabara ta kuɗancewa a cikin hamzari muka yi ba. Amma in kana sha'awar sanin yadda harkar ciniki ke tafiya da kuma yadda zaka iya shiga a dama da kai to ka da ka yi sake shirin Ji Ka Ƙaru ya wuce ka!

default

Harkar kasuwanci dai ta kankama a Afirka. Idan ka duba a gari ko ƙauyenku zaka ga harkar kasuwanci ta barbazu ko'ina. Mutane na ta saye da sayarwa a kasuwa ko su kafa tebura suna sayar da katunan wayar salula da abeban sha da kayan ƙwalama.

Amma a ɗaya hannun, akwai wata illa game da wannan ɓangare na abin da aka kira „kasuwanci marar rajista“. Saboda masu wannan harka ba sa samun kuɗaɗen shiga akai-akai, ba su da inshorar kiwon lafiya ballantana ma a yi batu game da kuɗin fansho.

A sabuwar salsalar shirin Ji Ka Ƙaru akan tattalin arziki zamu gabatar muku da wasu matasa su biyu, waɗanda suka tsayar da shawarar shiga harkar kasuwanci gadan-gadan. John da Jane dake da shekaru 16 da haifuwa 'yan biyu ne da suka rasa mahaifiyarsu kuma suke kai da komo tsakanin mahaifinsu da kakarsu. Wata rana, a lokacin hutu na makaranta, suka tsayar da shawarar kama wata harkar kasuwanci ta kansu. Zamu bi su sannu a hankali mu ga faɗi-tashin da suka fuskanta a harkarsu ta kasuwanci.

Sauti da bidiyo akan labarin