Mutane kusan 60 sun rasu a Afirka ta Tsakiya | Labarai | DW | 09.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane kusan 60 sun rasu a Afirka ta Tsakiya

Tashe-tashen hankula tsakanin sojojin sa kai da tsoffin 'yan tawayen ƙungiyar Seleka a ƙauyen Gaga na ci gaba da janyo asarar rayuka a ƙasar.

Kimamin mutane 60 aka kashe a rikice-rikicen ƙabilanci tsakanin sojojin sa kai da tsoffin 'yan tawaye a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Hakan dai na faruwa ne a daidai lokacin da ƙasar Faransa ke matsa ƙaimi da tsoma bakin ƙasashen duniya. Ƙasar mai arzikin ma'adanan ƙarƙashin ƙasa amma ke fama da talauci, ta tsunduma cikin ruɗani tun bayan da 'yan tawayen Seleka akasari Musulmi daga arewacin ƙasar suka kwace iko a birnin Bangui cikin watan Maris bayan sun hamɓarar da shugaba Francois Bozize. Shugaban riƙon kwarya Michel Djotodia ya rusa ƙungiyar 'yan tawayen amma gazawar gwamnatinsa wajen shawo kan rikicin ta sa gwamnatin Faransa kira ga Kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya da ya tura dakarun ƙasa da ƙasa don mayar da doka da oda. A ranar Litinin wasu sojojin sa kai sun kai hari a kan wuraren Seleka da ke ƙauyen Gaga inda suka kashe tsoffin 'yan tawaye hudu kafin su kai hari kan Musulmi fararen hula. Su ma mayaƙan Seleka sun mayar da martani a kan Kiristoci da ke kauyen.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdourahmane Hassane