1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhawara kan sojojin Jamus a Afghanistan

April 6, 2010

Sabuwar muhawara game da zaman sojojin Jamus a kasar Afghanistan

https://p.dw.com/p/Mobx
Sojojin Jamus a KundusHoto: AP

Wakilin musamman na majalisar dokokin taraiya a fannin tsaro, mai barrin aiki, Reinhold Robbe, yayi nuni da raunin dake akwai a bangaren baiwa sojojin horo da samar masu da kayan aiki. Sojojin guda ukku da suka mutu dukan su sojojin laima ne da suka fito daga Seedorf, a rundunar da Robbe ya kai mata ziyara jin kadan kafin a tura sojojin ta zuwa Afghanistan.. A lokacin wnanan ziyara, sojojin sun yi korafin cewr basu da isassun motoci, da zasu rika samun horo dasu, yadda zasu fuskanci aikin da za'a tura su yi a kasar ta Afghanistan. Wakilin na musaman na majalisar dokoi ya sake maimaita korafin da yayi a cikin rahoton sa na shekara, inda yace babu isassun motoci samfurin Dingo da Duro wadanda akan yi amfani dasu domin horad da matuka motocin rundunar ta sojan Jamus.

Wasu yan siyasar ma, sun kara maimaita kiran da suka yi ne game da cewar rndunar ta sojan Jamus cikin gaggawa tana bukatar jiragen saman yaki masu saukar ungulu da kuma na'urori na zamani na bincike da zasu yi amfani dasu a Afghanistan. Duk da haka, dan siyasar jam'iyar CDU, Ruprecht Polenz yace ya kara fahimtar yadda siyasa ke neman yin katsalandan a al'amuran soja. Yace bai kamata yan siyasa su zama kamar kwanandojojin soja. Ya amata ne su kyale al'amuran soja a hannun soja.

Yace ni kaina bani da wata masaniya game da wasu bukatu na musmaman na sojojin Jaus game da aiyukan su a Fghanistan, wadanda ba'a kula dasu a bisa masu su ba.. Ina da imanin cewar mun daurawa sojojin namu damar da ta dace, mun kuma basu isasshen horo, kafin a tura su ga wnanan aiki, domin babu mai iya daukar alhakin tura sojojin can ba tareda basu kayan aiki ko horon da ya dace ba.

Tsohon inspekta-janar na sojan Jamus, Harald Kujat yayi sukan cewar sojojin na Jamus a Afghanistan basu da na'urori na zamani na bincike, wanda saboda hakan ne suka fada mummunan dauki ba dadi da mayakan Taliban ranar Jumma'ar da ta wuce. To sai dfai ma'aikatar tsaro ta musunta wnanan zargi, tareda cewar rundunar sojan Jamus dai tana da isasshiyar damarar makamai, kuma sojojin da suka fada wanan dauki ba dadi sai da suka bincika yanknan da aka yi yakin a cikin sa tukuna.

Inspecta-janar na sojan Jamus, Volker Wieker yayi bayanin abin da ya sanya sojojin na kasa basu sami taimako ta hanyar jiragen saman yaki ba. Yace jiragen saman na yaki sun ki amfani da makamai ne saboda tsoron lafiyarf sojojin su da kuma al'ummar farar hula dake kusa.

Muhawara game da matsayin sojojojin a Afghanistan ya kama kama dai abu ne na al'ada. A duk lokacin da aka kashe sojojin Jamus a can, sabuwar muhawara takan barke, game da dacewa ko kuma karfin makamai da horon da sojojin suka dashi.

Muhawarar a wannan karo ta dauki wnaui sabon matsayi ganin cewar ministan tsaro, Karl Theodor zu Guttenberg yayi amfani da kalmar yaki a Afghanistan wanda a zahiri abu ne da tuni sojojin suke cikin sa a Afghanistan. Hakan ya kai ga tambayar ko ya dace a tura karin sojoji da kayan yaki zuwa kasar ta Afghanistan, domin yaki da yan Taliban. Ana dai sa ran cewar binciken da za'a gudanar a game da ainihin dalilin mutuwar sojojin guda ukku a Kundus, zai kai ga baiyana bukatar hakan.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita Nasiru Awal