Merkel ta fara tattaunawa da jam′iyyu | Labarai | DW | 07.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel ta fara tattaunawa da jam'iyyu

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce suna fatan za a cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin hadaka tare da jami'yyar 'yan gurguzu ta SPD.

Deutschland Sondierungsgespräche in Berlin Merkel und Schulz (Reuters/H. Hanschke)

Angela Merkel tare da shugaban jam'iyyar SPD Martin Schulz

Angela merkel ta bayyana haka ne a taron tattaunawar da aka soma a birnin Berlin tsakanin jam'iyyun siyasar domin yin sulhu don girka sabuwar gwamnati. Sama da watanni uku ke nan da yin zaben 'yan majalisun dokokin a Jamus sai dai har yanzu babu gwamnati. Tun da farko a cikin watan Nuwamba da ya gabata Angela Merkel ta yi kokarin ganin sun cimma yarjejeniya da jam'iyyun siyasa na FDP da masu kare muhali na Greens hakan ya gaggara.