1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel da May sun ziyarci Afirka

Mouhamadou Awal Balarabe
August 30, 2018

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Firaministar Birtaniya Theresa May sun kai ziyara a wasu kasashen Afirka ciki har da Najeriya da nufin karfafa huldar kasuwanci da diflomasiyya da ke tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/342m6
Theresa May Angela Merkel Bildkombo
Hoto: picture-alliance/dpa/W.Kumm/A.Rain

Theresa May ta Birtaniya ta je Afirka ta Kudu da Najeriya da Kenya domin samun kawayen da kasarta za ta yi cinikayya da su idan ta raba gari kwata-kwata da Kungiyar Tarayyar Turai. Ita kuwa Angela Merkel ta Jamus ta je Senegal da Ghana da Najeriya domin samar da mafita dangane da matsalar kwararar bakin haure zuwa Turai baya ga karfafa huldar tattalin arziki.