Merkel tana ziyara a wasu kasashen Afirka | Siyasa | DW | 29.08.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Merkel tana ziyara a wasu kasashen Afirka

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel tana soma ziyara a kasashen Najeriya da Ghana da Senegal. Batun bunkasa tattalin arziki na a sahun gaban muhimman batutuwan da za ta tattauna da kasashen a ziyarar.

Ga Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel wannan mako na zaman makon Afirka. A makonnin da suka gabata, shugabar gwamnatin Jamus din ta karbi bakuncin shugabannin kasashen Nijar da Angola a fadar gwamnati da ke Berlin. A yanzu kuma Merkel ta fara ziyara a kasashen yammacin Afirka. Ziyarar tata dai za ta mayar da hankali kan yadda za a bunkasa tattalin arzikin nahiyar Afirka. A wani faifen bidiyonta da ake yadawa duk mako, gabanin tafiyar tata Merkel ta nuna fata da kuma matukar farinciki tana mai cewa:

"Ina farinciki da cewa a mako mai zuwa zan yi tafiya zuwa Afirka. Ba wai kawai za mu mayar da hankali ne kan tattauna batun yin aiki tare wajen ayyukan raya kasa ba, har ma kan duk wani abu da ka iya tasowa, misali batun bude kofofin dangantakar tattalin arziki. Bangaren bunkasa tatalin arziki, batu ne da ke da matukar muhimmanci ga mafi yawan kasashen Afika, kasancewar su ne kasashen da ke tasowa. Suna da matasa masu yawa da ke bukatar samun horo da guraben ayyuka. A dangane da haka ya zamo wajibi mu sake karfafa dangantakar tatalin arziki da ke tsakaninmu da Afirka." 


Shin ko ya kwarru ke kallon dangantakare Jamus din da Afirka musamman ma bangaren dakile kwarar bakin haure?  A wata hira da ya yi da tashar DW Andreas Mehler da ke zaman kwararre kan Jamus da Afirka cewa ya yi:


"A bayyane yake karara cewa muhawara kan batun 'yan gudun hijira da bakin haure na kara zafi. Daga baki dayan kasashen uku, akwai ‚'yan cirani da ma bakin haure da ke shigowa ta haramtacciyar hanya. Hakan na zaman wani bangare na tushen ziyarar tata."

Sama da mutane dubu 11 ne daga wadannan kasashen uku suka nemi mafaka a Jamus a shekarar da ta gabata, sai dai wadannan kawai aka sani a hukumance. A yanzu haka akwai 'yan kasashen Ghana da Najeriya da kuma Senegal kimanin dubu 14 da ke zaune a Jamus, da aka yi watsi da takaddunsu na neman mafaka. Koda yake mayar da su din akwai wahala da kuma tsada kasancewar ofisoshin jakadancin Afirka da dama ba sa ba su Fasfo. Gwamnatin Tarayyar na ci gaba da neman hadin kan gwamnatocin Afirkan domin mayar da su gida. A yayin wata ziyara da Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya kai mata a Berlin, Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta shaida masa cewa suna son ganin mutanen sun koma gida domin radin kansu kafin su tilasta musu komawa. Sai dai da yake mayar da martani, Shugaba Akufo-Addo ya yi taka tsantsan, yana mai cewa suna son su tababbatar da cewa wadanda za a mayar din da gaske 'yan Ghana ne. 

A nasa bangaren Garba Kare mai fashin baki ne kan al’amuran da suka shafi siyasa a Tarayyar Najeriya, a cewarsa hanya guda ta magance matsalar bakin haure ita ce bunkasa tattalin arzikin Najeriya, wanda ya ce Jamus na da rawar takawa a awannan bangaren. Kare ya ce Jamus na iya taka rawa ta hanyar kasuwanci da zuba jari da tallafin raya kasa da ma sauran hanyoyi da Jamus din ka iya bi domin taimaka wa Najeriyar wajen dakile dubban mutane da ke bi ta Tekun Bahar-Rum da ma sauran hanyoyi domin shiga nahiyar Turai. Kan batun dangantakar kasuwanci kuwa Kare cewa ya yi:

"A matsayin kasa, Jamus ce ta fi cin gajiyar dangatakar kasuwancin da ke tsakanin kasashen biyu. Najeriya za ta so ta rinka cin gajiya sosai musamman ta la’akari da karfin tattalin arzikin da Jamus ke da shi, ganin cewa Najeriyar na bukatar tallafi a bangarori da dama a tattalin arzikin."

Kasashen Afirkan dai na da damar neman karin tallafi daga Jamus yayin ziyarar ta Merkel. Baya ga haka za su iya zawarcin karin kamfanonin Jamus masu zuba jari. A shekarar da ta gabata dai Jamus din ta yi alkawarin bai wa kasashen Afirkan tallafi, sai dai batun na yin tafiyar hawainiya.