Martanin nasarar jam′iyyar CDU a jihar NRW | Siyasa | DW | 15.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martanin nasarar jam'iyyar CDU a jihar NRW

A fagen siyasa a nan Jamus jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnati Angela Merkel ta yiwa babbar abokiyar hamaiyarta SPD mummunan kaye a zaben gunduma da aka gudanar na Jihar North rhein westphalia (NRW) a ranar Lahadi.

Jihar North rhein westphalia ita ce jihar da ke mafi yawan jama'a a Jamus a saboda haka zaben ya kasance mai matukar muhimmanci da daukar hankali da kuma ke zama zakaran gwajin dafi na babban zaben gama gari da za'a gudanar a bana. Jim kadan da baiyana sakamakon magoya baya a hedikwatar Jam'iyyar CDU a Düsseldorf da ke zama cibiyar jihar North rhein westphalia suka barke da tafi da murna.

Wannan nasara da jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ta samu dai na zama karin tagomashi ne ga nasarori biyu da jam'iyyar ta samu a zaben gundumomi na jihohin Saarland da kuma Schleswig Holstein

Da yake tsokaci Armin Lanchet na jam'iyyar CDU da zai zama sabon Firimiyan Jihar ta North Rheine Westphalia ya yi bayani da cewa: " Yau rana ce muhimmiya ga North rhein westphalia. Mun kudurce kudirori biyu a wannan zabe, mu dakatar da kawancen masu launin ja da kore, sannan mu zama babbar jam'iyya mai karfin tasiri, kuma mun cimma dukkan wadannan guda biyu. Ina gode muku bisa jajircewarku a wadannan kwanaki".

Ita dai SPD ta shafe kusan shekaru 46 tana mulkin Jihar ta North rhein westphalia da kuma ke zama mahaifar dan takararta Martin Schulz kafin shan kaye a hannun jam'iyyar CDU. Shan kayen kuma da ya kawo karshen mulkin na SPD a jihar ta North Rhein.    

Da ta ke jawabi Firimiyar jihar ta North Rhein Westphalia mai barin gado kuma 'yar takarar jam'iyyar SPD Hannelore Kraft ta ce sun gudanar da zabe a bisa manufa ta kuma taya murna ga dan takarar da ya yi nasara. " Ko kadan wannan sakamako bai yiwa jam'iyyar Social Demokrat a wannan jiha ta North rhein westphalia dadi ba."

Shi ma dai Martin Schulz na jam'iyyar ta SPD da zai kalubalanci Angela Merkel a mukamin shugaban gwamnati bai yi kasa a gwiwa ba wajen amincewa da shan kaye tare kuma da taya abokan hamaiyarsa murna.

Jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ta sami nasara a zaben da kashi 33 cikin dari na kuri'un da aka kada yayin da SDP ta sami kashi 30 cikin dari. Sauran jam'iyyun da suka fafata a zaben su ne FDP wadda ta sami 12.1 cikin dari sai AfD mai akidar kyamar baki da ta sami kashi 7.6 cikin dari na kuri'un. Sai dai kuma jam'iyyar ta sami nasarar wakilci a majalisun dokokin jihohi 13 na tarayyar Jamus.

 

Sauti da bidiyo akan labarin