Majalisar dokokin Syria ta bayyana kalaman Khaddam da cewa cin amanar kasa ne | Labarai | DW | 31.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar dokokin Syria ta bayyana kalaman Khaddam da cewa cin amanar kasa ne

A wani kuduri da ya samu goyon bayan dukkan ´yan majalisar dokokin Syria, an bayyana kalaman da tsohon mataimakin shugaban kasar Abdel Halim Khaddam yayi da cewa cin amanar kasa ne. Kudurin ya bayyana furucin da mista Khaddam yayi na rawar da Syria ta taka dangane da kisan tsohon FM Lebanon Rafik Hariri da cewa babban cin amanar kasa ne. Shi dai Khaddam ya fadawa tashar telebijin ta Al-Arabiya cewar shugaban Syria Bashar al-Assad ya yi amfani da kalamai masu tsauri wajen razana tsohon FM na Lebanon kafin a halaka shi a cikin watan fabrairu. Tsohon mataimakin shugaban ya ce zai yi wuya a ce hukumar leken asirin Syria ra shirya wannan kisa ba tare da sanin shugaba Assad ba. A cikin rahotonsa, mai binciken wannan kisa a madadin MDD kuma mai shigar da kara na Jamus Detlev Mehlis ya zargi jami´an leken asirin Syria da hannu a kisan na mista Hariri.