Majalisar dokokin Jamus ta amince da shirin doka dangane da dokokin mafakar siyasa | Labarai | DW | 15.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar dokokin Jamus ta amince da shirin doka dangane da dokokin mafakar siyasa

Kudurin dokar ya tanadi sanya kasashen Albaniya da Kosovo da Montenegro a jerin yankuna masu kwanciyar hankali, da gaggauta duba bukatun masu neman mafakar siyasa.

Deutschland Bundestag Angela Merkel Wolfgang Schäuble und Thomas de Maiziere

Angela Merkel da Wolfgang Schäuble (hagu) da Thomas de Maiziere

Da gagarumin rinjaye majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta amince da shirin doka na dokokin mafakar siyasa da 'yan gudun gudun hijira. Kudurin dokar ya tanadi sanya kasashen Albaniya da Kosovo da Montenegro a jerin yankuna masu kwanciyar hankali, da gaggauta duba bukatun masu neman mafakar siyasa hade kuma da fadada matakan shigar da 'yan gudun hijira da ke da kyakkyawar damar samun izinin ci-gaba da zama a Jamus, cikin al'ummar kasar. A ranar Jumma'a za a gabatar da kudurin dokar gaban majalisar wakilan jihohin tarayya, sannan a fara aiki da dokar a ranar 1 ga watan Nuwamba. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi tsokaci kan shirin dokar tana mai cewa:

"An kammala wannan shirin doka cikin kankanen lokaci, daga ranar 1 ga watan Nuwamban wato kasa da wata guda za mu inganta dokokinmu da suka shafi masu shigowa kasar nan saboda dalilan tattalin arziki, za mu gaggauta tasa keyarsu, domin ba wa wadanda suka cancanta damar samun taimakon da suke bukata."