Kura ta fara lafawa bayan harin Kamaru | Labarai | DW | 12.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kura ta fara lafawa bayan harin Kamaru

Hankula sun fara kwanciya a Kamaru bayan da aka yi wata taho mu gama tsakanin sojin kasar da 'yan Boko Haram kan iyakar kasar da Najeriya.

Wata majiya ta rundunar 'yan sanda kasar ta ce 'yan Boko Haram ne da sanyin safiyar Litinin suka tinkari sansanin sojin na Kolofata da ke lardin arewa mai nisa inda suka yi kokarin karbe iko da shi amma sai suka fuskanci tirjiya wanda ya hana harin nasu ya yi tasiri.

Wannan farmakin dai ya sanya mazauna yankin tserewa zuwa wasu wuraren da ke makota don tsira da rayukansu. Harin dai na zuwa ne bayan da a kwanakin baya kungiyar ta Boko Haram ta karbe iko da wani sansanin soji na kasa da kasa da ke kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Chadi.