Kungiyyar yan tawayen Chadi ta lashi takobi... | Zamantakewa | DW | 12.04.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Kungiyyar yan tawayen Chadi ta lashi takobi...

Harkokin zaman lafiya sun kara dagulewa a gabashin kasar Chadi

default

Ya zuwa yanzu dai tuni, kungiyyar hadin kann kasashen Africa, wato Au tayi Allah wadai da wannan hari da kungiyyar yan tawayen ta Chadi ta kai izuwa sansanin yan gudun hijira da yayi iyaka da yankin Darfur na kasar Sudan daga gabashin kasar ta Chadi.

A cewar shugaban hukumar zartarwa na kungiyyar ta Au, wato Alpa Omar Konare, matakin kai harin da kungiyyar yan tawayen ta dauka,abu ne daya yi karan tsaye ga dokar kasa da kasa, a don haka ya zama wajibi a cewar sa yan tawayen su tattara nasu ya nasu su fice daga yankunan da suka kutsa a cikin su.

Mr Konare, wanda ya fadi hakan a yau laraba, ya tabbatar da cewa akwai bukatar gwamnatin kasar ta Chadi ta koma teburin sulhu da kungiyoyin yan tawayen don nemo bakin zaren warware wanmnan rikici ta hanyar ruwan sanyi.

Har ilya yau, shugaban hukumar zartarwar kungiyyar ta Au, ya kuma yi Allah wadai da duk wani yunkuri na kungiyyar yan tawayen wajen kifar da halastacciyar gwamnatin kasar ta Chadi karkashin shugaba Idiris Debby, da cewa hakan ya sabawa doka ta kasar da kuma dokokin kungiyyar ta Au.

A game kuwa da kasashen Africa kuwa , Mr Konare cewa yayi kungiyyar Au, ba zata lamunci hambarar da gwamnatin da aka zaba ba ta hanyar dimokradiyya ta amfani da karfin tuwo, ko kuma wani abu mai kama da haka, a don haka idan akwai wata matsala kamata yayi a warware ta ta hanyar tattaunawa amma bata hanyar tashin hankali ba.

Ya zuwa yanzu dai kafafen yada labaru sun rawaito ministan tsaro na kasar ta Chadi na fadin cewa, dakarun sojin su sun samu galabar kwato garin Mongo dake gabashin kasar,daga hannun yan tawayen.

Game da hakan kuwa tuni kungiyyar yan tawayen ta karyata wannan furuci da ministan tsaron kasar yayi, da cewa har yanzu dakarun su ne ke rike da ragamar tafiyar da harkoki a garin na Mongo.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa, kungiyyar yan tawayen ta FUT, ta kasance mai kaddamar da hare hare a gabashin kasar ta Chadi,inda a yan kwanakin nan abin yayi tsamari, wanda hakan ya kara haifar da tsugune tashi a kokarion da ake na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Yankin dai da kungiyyar yan tawayen ke kai ire iren wadannan hare hare, ya kasance yaki ne da Mdd ta tanadarwa yan gudin hijira, wanda kuma a nan ne garin na Mongo yake.

 • Kwanan wata 12.04.2006
 • Mawallafi Ibrahim Sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvTe
 • Kwanan wata 12.04.2006
 • Mawallafi Ibrahim Sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvTe