1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar G8 ta yi alƙawarin ba Afirka tallafin dala miliyan dubu sittin

Mohammad Nasiru AwalJune 8, 2007

Za´a yi amfani da tallafin wajen yaki da cutar AIDS, Malaria da kuma TB.

https://p.dw.com/p/BtvN
Merkel da Kufour na Ghana
Merkel da Kufour na GhanaHoto: AP

Kasar Amirka ce zata ba da kashi 50 cikin 100 na kudaden taimakon da aka yi alkawarin ba wa Afirka don ta yaki cutar AIDS ko Sida da zazzabin cizon sauro malaria da kuma tarin fuka wato TB. Tun gabanin taron kolin kungiyar G8 a Heiligendamm shugaban Amirka GWB ya ba da wannan sanarwa. Sauran dala miliyan dubu 30 din kuwa sauran kasashe 7 masu arzikin masana´antun ne zasu bayar. A cikin shekaru 8 masu zuwa Jamus zata ba da Euro miliyan dubu 4. Wato kenan gwamnatin Jamus zata kara yawan kasafin kudin taimakon raya kasashe masu tasowa da misalin Euro miliyan 500. Tuni kuwa har SGJ Angela Merkel da ministar ba da taimakon raya kasa Heidemarie Wieckzorek-Zeul sun amince su kara kasafin da Euro miliyan 750 daga shekara mai zuwa. Wato Afirka zata samu karin taimako na Euro miliyan 250.

Hakan kuwa yana da muhimmanci don samun sukunin cika alkawarin da aka dauka a taron Gleneagles na Scotland shekaru biyu da suka wuce. A wannan taron kasashe masu karfin arzikin masana´antu sun yiwa kasashen Afirka alkawarin rubanya yawan taimakon raya kasa zuwa dala miliyan dubu 50 a kowace shekara har zuwa shekara ta 2010. To sai dai har yanzu ana nesa da cika wannan alkawari. Bayan ganawar da aka yi da shugabannin Afirka a zauren taron na Heiligendamm SGJ Angela Merkel ta nunar da cewa.

1. O-Ton Merkel:

“Alhakin da ya rataya wuyan kungiyar G8 shi ne zamu cika alkawarin da muka dauka. Ko shakka babu zamu yi haka. A daya bangaren kuma muna bin diddigin abubuwan dake wakana a Afirka. Kawayen mu na Afirka sun fada mana cewar muna iya yin bincike akan nasarori ko akasin sa da aka samu.”

Merkel ta ce za´a gabatar da wani rahoto bisa wannan manufa tare tattaunawa da wakilan kasashen Afirka a taron kolin G8 na badi da zai gudana a garin Toyako na Japan. Daga cikin shugabannin Afirka da suka halarci taron na Heiligendamm akwai shugaban Algeria Abdelaziz Bouteflika da Abdulaye Wade na Senegal da shugaban kungiyar tarayyar Afirka John Kufour na Ghana da Umar Musa ´Yar Adua na Nigeria da kuma shugaban hukumar AU Alpha Omar Konare. Bayan taron shugaban Ghana John Kufour ya nunar da cewa.

2. O-Ton Kufour:

“Afirka na sa rai kawayenta na G8 zasu cika alkawuran da suka dauka. Mu kuma a namu bangaren mun dauwa kanmu nauyin yin duk abubuwan da suka wajaba don samun wata dangantaka ta gaskiya a tsakani. Mun ba da shawarar kafa wata hukuma wadda zata rika yin bincike kan cika alkawuran.”

A dai halin da ake ciki shugabannin mayan kasashe masu arzikin masana´antu da takwarorinsu na Afirka sun kuduri aniyar karfafa hadin kai tsakani sakamakon tattaunawar da suka yi a Heiligendamm. Sanarwar da suka bayar ta ce za´a kafa wata dangantaka kwakkwara tsakanin kungiyar G8 da Afirka.