koriya ta arewa tace banda japan a tattaunawar nucleanta | Labarai | DW | 04.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

koriya ta arewa tace banda japan a tattaunawar nucleanta

Koriya ta arewa ta gargadi kasar Japan da kada ta shiga tattaunawar kasashe shida akan tattauna kawo karshen harkokin nuclearn Pyongyang da zaa gudanar.Wani jamiin kasar ta koriya ta Arewa ya bayyana Japan da kasancewa yar koren Amurka,wadda ake amfani da ita a matsayin karen farautar siyasa.A shekarata 2003 nedai aka kaddamar da taron farko na kasashe shida akan shirin Nuclearn koriya ta arewan,taron daya hadar da koriyoyin biyu, da Amurka da Sin da Rasha da kuma ita Japan.