Kokarin magance rikicin gabashin Ukraine | Labarai | DW | 08.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin magance rikicin gabashin Ukraine

Kasashen Faransa da Jamus, sun dukufa na ganin an samu cimma yarjejeniya mai dorewa kan rikicin gabashin Ukraine, inda tun daga ranar Alhamis ake kokarin samun mafita.

A kokarin da ake na shawo kan matsalar rikicin gabashin Ukraine, an shirya gudanar da wani babban zaman taro da zai samu halartar kasashen Faransa, Jamus, Ukraine da Rasha a ranar Laraba mai zuwa a birnin Minsk na Belarus. Wannan labarin ya fito ne a wannan Lahadin daga Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel bayan wata mahawara da suka yi tsakanin shugabannin hudu ta wayar tarho.

Shugabannin dai da suka hada da ta Angela Merkel ta Jamus, da François Hollande na Faransa, da Petro Porochenko na Urkaine da kuma Vladimir Poutin na Rasha sun dauki lokaci mai tsawo da safiyar wannan Lahadin suna tattaunawa ta wayar tarho kan matsala gabashin kasar ta Ukraine, inda a ranar Litinin ce za su ci gaba da wannan aiki da suka soma a Berlin babban birnin kasar Jamus a kokarin samar da mafita ta dindindin kan rikicin gabashin na Ukraine.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mohammad Nasiru Awal