Kisan mutane a wani kauyen jihar Borno | Labarai | DW | 05.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kisan mutane a wani kauyen jihar Borno

Mutane sama da 40 ne suka rasu a garin Njaba da ke daura da Damboa kana yake da tazarar kilomita 100 kudu da Maiduguri a jihar Borno da ke arewacin Jajeriya.

Masu aiko da rahotanni suka ce da asubahin ranar Talatar da ta gabata ce wasu 'yan bindiga da ake zaton 'yan kungiyar nan ce ta Boko Haram suka afkawa wasu gidaje da ke kauyen inda suka yi ta harbin kan gidajen mutane.

Wani jami'i rundunar sojin Najeriya a Maiduguri ya ce labarin harin bai kai gare su ba sai yau saboda yankin cikin kauye sosai, dalilin da ya hana jami'ansu kai dauki.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da kasashen Kamaru da Chadi da Nijar ke dafawa Najeriya a kokarin da ake na kawo karshen hare-haren 'yan kungiyar.