1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kira ga hadin kan Najeriya da makwabtanta

December 16, 2014

Ministan tsaron kasar Faransa ya yi kira bisa hulda tsakanin Najeriya da sauran kasashe makwabtanta na Nijar, Cadi, da kuma Kamarun wajen yakar 'yan kungiyar Boko Haram

https://p.dw.com/p/1E5LX
Hoto: AFP/Getty Images/N. Tucat

Da yake magana yayin babban taro kan zaman lafiya da ke gudana a birnin Dakar na kasar Senegal, ministan tsaron na Faransa Jean-Yves Le Drian, ya kara da cewa akwai babbar barazana ga mutuncin kasar Najeriya da sauran kasashe makwabtanta, kuma kasar Faransa na goyon bayan kokarin da wadannan kasashe ke yi na ganin sun hada karfi da karfe domin kawo karshen wannan matsala ta ta'addanci ta hanyar kafa runduna guda ta hadin gwiwa, inda ya ce a shirye suke su bayar da taimakon manyan sojoji da za su taimaka wa rundunar.

Tun farko dai an yi bayanin cewa kasashen za su tura sojoji kimanin 2,800 a iyakokinsu da Najeriya kafin karshen watan Nowamba da ya gabata, amma kuma har yanzu ba'a samu kai ga kafa wannan runduna ba, yayin da 'yan kungiyar ta Boko Haram ke ci gaba da ayyukan ta'addanci a kasar ta Najeriya da ma makwabtanta a cewar sa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Suleiman Babayo