Kasar Chadi ta soki Najeriya | Labarai | DW | 27.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasar Chadi ta soki Najeriya

Shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya zargi Najeriya da yin rikon sakainar kashi ga barazanar kungiyar Boko Haram da kuma kin bada hadin kai a yaki da kungiyar.

Deby ya bayyana hakan ne ga wata mujalla ta kasar Faransa mai suna Le Point, yayin wata tattaunawa da suka yi da shi cikin wannan mako, inda ya ce babu wata alaka tsakanin sojojin kasashen da ke cikin rundunar hadakar da kuma na Najeriyar. Tun dai a watan Janairun da ya gabata ne kasashen Chadi da Kamaru da kuma Jamhuriyar Nijar suka hda karfi waje guda tare da samar da rundunar sojojin da ke yakar kungiyar ta Boko Haram da hare-harenta da ta ke kaiwa ya yi sanadiyyar asarar rayuka sama da 13,000 tun daga shekara ta 2009. Deby ya bayyana takaicinsa na cewa har yanzu babu wani mataki daga bangaren gwamnatin Najeriya kana basu ji komai ba daga rundunar sojojin Najeriya.