Kamaru ta ce za ta kawar da Boko Haram | Labarai | DW | 13.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kamaru ta ce za ta kawar da Boko Haram

Shugaban Jamhuriyar Kamaru Paul Biya ya ce gwamnatinsa za ta matsa kaimi waje yaki da 'yan kungiyar nan ta Boko Haram domin ganin ta kawar da kungiyar.

Mr. Biya ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin mutane 27 ciki kuwa har da mai dakin mukaddashin firaministan kasar wanda aka sace su a makonnin da suka gabata.

Shugaban na Kamaru ya ce "gwamnatin Kamaru za ta cigaba da kokari wajen yakar Boko Haram har sai ta ga bayan kungiyar baki daya."

Daga cikin mutanen da suka kubuta daga hannun 'yan Boko Haram din dai akwai 'yan Kamaru 17 da kuma wasu 'yan asalin kasar China su 10, lamarin da ya sanya China din ta bakin jakadanta da ke Kamarun Wo Ruidi cewar za ta bada tallafinta ga Kamaru da sauran kasashe wajen ganin an yaki ta'addanci.