1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Johannes Rau shugaban tarayyar Jamus mai barin gado.

Mohammad Nasiru AwalMay 14, 2004
https://p.dw.com/p/BvjZ
Johannes Rau lokacin da yake jawabin sa na karshe a matsayin shugaban Jamus.
Johannes Rau lokacin da yake jawabin sa na karshe a matsayin shugaban Jamus.Hoto: AP

Daukacin Jamusawa na tattare da ra´ayin cewa Johannes Rau adilin shugaba ne. Alkalumma sun yi nuni da cewa kashi 70 cikin 100 na al´umar wannan kasa sun gamsu da shugabancin Rau a matsayin wani shugaba mai tausayin al´aumarsa. Kamar magabatansa, Rau ya dauki kansa a matsayin shugaban Jamusawa da kuma baki da ke zaune a wannan kasa ba tare da nuna bambamcin akidar siyasa ba.

Jim kadan bayan an zabe shi a wannan mukami a ran 23 ga watan mayun shekara ta 1999, Rau ya tare a fadar sa dake birnin Berlin, kuma tun sannan ya kama aikinsa na bautawa al´umar wannan kasa kamar yadda sashe na 56 na kundin tsarin mulkin tarayyar Jamus ya nunar. To sai dai yanzu duniya ta tashi daga wannan tsari, musamman idan aka yi la´akari da yawan baki kimanin miliyan 8 dake zaune a wannan kasa. Kuma kamar takwarorinsu Jamusawa, su ma suna aiki tare da biyan haraji.

Johannes Rau ne shugaban Jamus na farko dake magana da yawun dukkan al´umomi dabam-dabam dake wannan kasa, kuma yake cika alkawarin da ya dauka musu. Shi dai shugaban ya na da ra´ayin cewa sai an yi sha´awar al´adu da addinai da kuma halin rayuwar bakin da ke zaune a wannan kasa ne sannan za´a iya samun wani yanayi na yarda da juna don samun kyakkyawar zamantakewa tsakanin bakin da kuma ´yan kasa. Gudummawar da ya bayar wajen cimma wannan matsayin na daga cikin muhimman abubuwan da suka sa ake kaunar sa a wannan mukamin na shugaban tarayyar Jamus.

To wai mai yasa wasu musamman daga cikin masu fada a ji na wannan kasar suka tsane shi? Watakila dai hakan ba zai rasa nasaba da wani abin kunya game da tafiye-tafiye ta jirgin sama ba bisa ka´ida ba da yayi a lokacin da yake rike da mukamin Firimiyan jihar North Rhein Westfalia.

A cikin jawabinsa na biyar kuma na karshe shugaba Rau ya soki lamirin shugannin siyasa da na manyan kamfanoni a wannan kasa. Rau ya yi korafin cewa magabatan wannan kasa na nuna son kai da nuna halin ko-in-kula ga matsalolin da talakawa ke ciki. Ko shakka babu wadannan kalaman tamkar sosawa talakawan wannan kasa inda ke yi musu kaikayi ne. Shi dai Rau ya kasance mai sadaukar da kansa ga bukatun talakawa musamman a wannan lokaci da ake fuskantar matsalolin yawan marasa aikin yi da kuma barazanar ayyukan ta´addanci. Rau ya tabo batutuwan dake ciwa mutane tuwo a kwarya kamar na kwararar baki, manufar hade manufofin kasuwancin duniya bai daya da kuma na binciken sauya kwayoyin halittu. A duk inda ya kai ziyara ko dai a Afirka ko Latunamirka ko kuma Asiya, shugaban na samun kyakkyawar tarba. Rau dai ya kasance wani gwarzon shugaba, wanda daukacin mazauna nan Jamus ke kaunarsa ba don komai ba sai saboda kwarewarsa wajen sanin inda aka sa gaba.