1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Cece kuce kan sakamakon zaben kasar Zambiya

Mohammad Nasiru AwalAugust 19, 2016

Sakamakon zaben Zambiya da kisan gillan da aka yi a garin Beni na gaashin Kwango da sake bullar cutar Polio a Najeriya sun dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/1JlYv
Sambia Anhänger von Edgar Lungu nach den Wahlen in Lusaka
Hoto: Reuters/Jean Serge Mandela

Za mu fara sharhi da labaran jaridun na Jamus game da nahiyarmu ta Afirka da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda ta leka kasar Zambiya tana mai cewa da kuri'u kadan ne shugaban kasa Edgar Lungu ya kada dan takarar adawa Hakainde Hichilema a zaben shugaban kasar na makon da ya gabata.

Jaridar ta ce tuni dai dan adawa ya zargi shugaban kasar da gama baki da hukumar zabe don yin aringizon kuri'u kana ya sanar cewa zai daukaka kara a gaban kotun kundin tsarin mulkin kasa don kalubalantar sakamakon zaben. Akalla mutane 150 jami'an tsaron kasar ta Zambiya suka tsare a kudancin kasar bayan sun gudanar da zanga-zangar adawa da sake zaben shugaba Edgar Lungu.

Tabarbarewar lamuran tsaro a gabashin Kwango

Al'umma ta yi boren kin tashin hankali inji jaridar Die Tageszeitung tana mai mayar da hankali kan wata zanga-zangar da aka yi a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango bayan kisan gillan da aka yi a garin Beni.

Kongo Beni Menschenmenge nach Massaker
Al'ummar Beni na nuna fushinsu bayan wani kisan gillaHoto: Getty Images/K.Maliro

Jaridar ta ce fushin al'umma a gabashin Kwangon bayan kisan mutane da dama a garin Beni ya yi yawa, inda a ranar Laraba mutane masu dinbim yawa da a garesu gwamnati ce ke da alhakin tabarbarewar lamuran tsaro a yankin, suka gudanar da zanga-zanga. 'Yan sanda sun yi kokarin amfani da hayaki mai sa hawaye da harbi cikin iska don tarwatsa masu zanga-zangar da akasari matasa ne, har sai da gas din mai sa hawaye ya kare. An dai harbe matashi guda har lahira. A daren Asabar zuwa wayewar garin ranar Lahadi wasu 'yan bindiga sanye da kayann sojojin Kwango suka yi wa mutane fiye da 50 kisan gilla a kusa da garin na Beni. Gwamnati a birnin Kinshasa ta zargi 'yan tawayen kungiyar ADF da ke aika-aikarta a kan iyakar Yuganda da Kwango da aikata ta'asar.

Cin zarafin ma'aikatan agaji a Juba

Kakkausan suka kan gwamnatin Sudan ta Kudu inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung.

Südsudan UN denken über Verstärkung von Unmiss nach
Za a kara yawan sojojin duniya a JubaHoto: Reuters/A. Ohanesian

Ta ce ana zargin dakarun gwamnatin Sudan ta Kudu da laifin yi wa mata da yawa ma'aikatan kungiyoyin agaji na kasa da kasa fyade jim kadan bayan fadan da sojojin gwamnatin suka yi da 'yan tawaye a birnin Juba a farkon watan Yuli, kuma a kan idonsu sojojin suka harbe wata 'yar jarida 'yan kasar ta Sudan ta Kudu har lahira. Wadanda lamarin ya shafa sun shaida wa kamfanin dillancin labarun AFP cewa ko da yake sun sanar da tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ke a Juba da kuma ofishin jakadancin Amirka wannan labari, amma ba wanda ya kai musu dauki. Yanzu haka dai babban sakataren MDD Ban Ki Moon ya ba da umarnin gudanar da binciken zargin da ake wa dakarun MDD da rashin kai wa ma'aikatan agajin taimako.

Cutar Polio ta sake bulla a Najeriya

A karshe sai jaridar Die Tageszeitung wadda ta ce ci gaban da aka samu a kokarin baya-bayan nan na kakkabe cutar Polio daga duniya ya gamu da cikas, bayan da gwamnatin Najeriya da kuma hukumar lafiya ta duniya WHO suka tabbatar da sabbin wadanda suka kamu da kwayoyin cutar a kasar na farko cikin shekaru biyu. Ta ce a shekarar 1988 mutane dubu 350 a kasashe 125 ke dauke da Polio, amma kokarin duniya na kawar da annobar, ya biya domin a shekarar 2015 mutane 74 ne kawai aka tabbatar suna da Polio a kasashe biyu wato Afghanistan da Pakistan. A watan Nuwamban bara aka ayyana Najeriya a matsayin kasar Afirka ta karshe da ta kawar da Polio.