Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Zambiya tana cikin kasashen kudancin Afirka da Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka kafin zama Jamhuriya a shekarar 1964.
Zambiya tana cikin kasashen Afirka da suke da kwarya-kwaryar zaman lafiya. Lusaka ke zama babban birnin kasar ta Zambiya.
Rikicin siyasa kasar Mali da batun dangantakar Rasha da Afirka ta Kudu ya zuwa kamarin matsalar sace-sacen yara da mata a kasar Zambiya, su suka dauki hankalin jaridun Jamus a wannan makon.
Zambiya na shirin sake gina hanyar Lusaka zuwa Ndola mai tsawon kilomita 327, a wani aiki da ake sa ran zai lakume sama da dalar Amurka miliyan 577.
Watanni bakwai bayan da asusun bayar da lamuni na duniya IMF ya amince zai tallafa wa kasar Zambia da kudade dala biliyan $1.3 har yanzu hukumomin kasar sun gaza cika sharudan samun tallafin.
A cikin shirin za a ji cewa, a Jamhuriyar Nijar gwamnati na kokawa kan yadda ake kara samun yawan adadin yara da ke bara a titunan manyan biranen kasar. Shi kuwa shugaban kasar Zambiya na ci gaba da shan suka kan yawan balaguron da yake yi zuwa kasashen ketare.
Shirin na kunshe da rahotanni da labarai daga bangarori dabam-dabam na duniya.
A Najeriya ana martani a kan gargadin da ofisoshin jakadancin Amurka da Birtaniya da na Italiya suka yi a kan yiwuwar kai hare-haren ta’adanci a Abuja. Masana kimiyya a Jmaus sun danganta fatara da matsalolin tabin hankali da wasu kan shiga.
Kungiyar tattalin arzikin yammacin Afrika ta katse takunkumin da aka kakaba wa Mali watanni shida baya sakamakon jan kafa wajen shirya zabe. Wasu jaridun Jamus sun dubi wannan.
Shugaba Hakainde Hichilema na kasar Zambiya ya bayyana sadaukar da albashinsa na kowani wata a bangaren illimin kasar da ma taimakon marasa galihu.
Masanan sun shawarci a bai wa 'yan kasa dama ta hanyar sassauta kudaden shiga wuraren shakatawa da bude ido idan ana son bunkasa wannan fannin a Afirka.
Za a ji gwamnatin kasar Zambiya ta fara shirin siyan tattacen man fetur daga makwafciyarta Angola.
Wata kotu a kasar Afirka ta Kudu, ta yanke wa mai horas da 'yan wasan kwallon kafa na kasar Uganda Milutin Sredojevic hukuncin shekaru uku a gidan yari bayan samunsa da laifuka biyu na cin zarafi.
A wannan mako jaridun Jamus sun dubi nasarar Hakainde Hechilema a Zambiya da batun bai wa 'yan Afghanistan mafaka a Yuganda.
Zababben shugaban kasar Zambiya Hakainde Hichilema ya yi alkawarin mutunta hakkin duk 'yan kasar kuma babu ramuwar gayya kan cin zarafin da ya fuskanta daga hannun gwamnati mai barin gado.
Shugaba Edgar Lungu ya taya Hakainde Hichilema abokin hamayyarsa murna bayan da ya amince da shan kaye a babban zaben kasar da ya gudana a makon jiya.
Hukumar kula da zabe a Kasar Zambiya ta sanar da cewar jagoran 'yan adawa Hakainde Hichilema ya samu nasara da gagarumin rinjaye a zaben shugaban kasar da aka yi a makon jiya a gaban shugaba mai barin gado Edgar Lungu.