Zambiya: Mafita kan bashin IMF da China | Siyasa | DW | 30.03.2023
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zambiya: Mafita kan bashin IMF da China

Watanni bakwai bayan da asusun bayar da lamuni na duniya IMF ya amince zai tallafa wa kasar Zambia da kudade dala biliyan $1.3 har yanzu hukumomin kasar sun gaza cika sharudan samun tallafin.

IMF dai ta bukaci Zambiya ta rage alaka da China tare da shawo kan China ta sassauta wa kasar basukan da take bin ta. Tuni dai wannan lamari ya haifar da zazzafar muhawara a cikin kasar. Jam'iyyar adawa ta Republican a Zambiya ce dai ke kan gaba wajen matsa wa gwamnati lamba kan batun, inda shugaban jam'iyyar Wright Musoma ya ce idan har hukumomin kasar na son nemar wa kasar makoma ta gari, ya zama wajibi su mutunta China a maimakon biye wa kasashen yamma da a cewarsa, ke kokarin kai kasar su baro. Dan siyasar ya zargi shugaba Hakainde Hichilema da hada baki da kasashen yamma, lamarin da ya ce ya jefa kasar cikin mawuyacin hali.

Abin ya kai har ana umartar kasarmu da ta rage ko kuma ta daina alaka da China da Rasha, an manta cewa wadannan kasashen sun kasance a tare da mu a lokacin da muke neman taimako. A lokacin da kasashen yamma suka yi wa kakanninmu mulkin mallaka, Rasha da China ne dai suka ciyar damu abinci, suka kuma taya mu fada wajen yakar su. Har yanzu ma wadannan kasashen na ilmantar da yaranmu ba tare da sun biya wani abu da ya taka kara ya karya ba.

Shugaban kungiyar Zambiya Debt Alliance mai sanya ido kan basukan da kasar ke karbowa Peter Mumba ya ce siyasar da ake amfani da ita a game da batun sauya fasalin basukan da China ke bin Zambiya, na kawo rudani a kasar. Ya ce bincikensu ya nuna musu cewa akwai sarkakiya dangane da al'amarin.

China ta kasance abokiyar kirki ga Zambia. Mun ga yadda China ta shiga ta fita wajen saukaka wa kasar nan yawan bashin da ake bin mu. A saboda haka, mu shawarar mu ita ce kada Zambiya ta hada kai da wata kasa hatta ga batun sauya fasalin basukan da ake magana a kansu. Muna kuma kira ga wadanda ke bin mu bashi da su kalli kokarin da muke yi su sassauta mana.

Shugaban kasar Zambiya Hakainde Hichilema

Shugaban kasar Zambiya Hakainde Hichilema

To sai dai a cewar masanin tattalin arziki Alexander Nkosi a tsakanin kasashen yamma da China da Rasha babu wani dan goyo a cikinsu domin kowannensu ya bai wa wasu kasashen Afirka ba shi. Ya ce manyan kasashen na bai wa Afirka basuka domin su sami damar mallaka ko kuma kwasar ma'adanan karkashin kasa na Afirka a fakaice.

Dabararsu ita ce su matsa wa China lamba ta amince ta saukaka basukan da take bin Zambiya, kuma ita China ta gano hakan. Hukumomin na China suna cewa eh, mun yarda muna bin Zambiya bashi amma kuma kasahsen yamma kuna bin ta, a saboda haka, idan har za a yi wani sassaucin ko sauya fasalin wani bashi da wata kasa ke bin Zambiya kamata ya yi ku ma kasashen yamma ku yi hakan.

Masana dai na cewa mafita ita ce mahukuntan Zambiya su hau teburin tattaunawa da na China domin duba yadda za a saukaka basukan da ake bin Zambiya. To amma wasu na cewa dasawar da shugaban Zambiya ke yi da kasashen yamma a maimakon China da Rasha ka iya haifar da shakku a zukatan jami'an China, inda wasu ke ganin da shugaban na Zambiya zai wanke kafa ya je China da watakila hukumomin Beijing sun saukaka wa kasar tarin bashin da aké bin ta.

 

Sauti da bidiyo akan labarin