Asusun Bada Lamuni na duniya wato IMF asusu ne da ke tallafawa wajen ganin kasashen duniya sun tsaya da kafafunsu, inda mafi akasari ya kan tallafa musu ta fuskar tattalin arziki.
Asusun IMF kan yi aiki da nufin ganin kasashen duniya da ke fuskantar kalubale na tattalin arziki sun samu waraka. Asusun kan tallafa musu da kudi wajen yin aikinsu na yau da kullum. Yanzu haka dai Asusun na da hedikwatarsa ne a birnin Washington DC na Amirka.