Jamus za ta fadada dangantaka da Chadi | Siyasa | DW | 13.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jamus za ta fadada dangantaka da Chadi

Batun tsaron yankin tafkin Chadi da kasancewar Jamus a Afirka da matsalar kasar Libiya sun mamaye tattaunawa tsakanin Angela Merkel da Idriss Deby.

Shugaban kasar Chadi Idriss Deby Itno da ya kawo wata ziyarar aiki a nan Jamus, ya gana da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a Berlin babban birnin kasar. Shugaban na Chadi wanda kuma yake shugaban kungiyar Tarayyar Afirka, ya tattauna batutuwa da dama da suka shafi kasancewar Jamus a Afirka, da batun tsaro a yankin tafkin Chadi da kuma matsalar kasar Libiya. Sai dai a hannu daya 'yan kasar ta Chadi da ke zaune a Jamus sun yi tasu zanga-zanga kan wannan ziyara.

A tattaunawar da ya yi da tashar DW jim kadan bayan ganarwarsa da Angela Merkel, Shugaba Idriss Deby Itno ya yi tsokaci kan wannan ziyara tashi da kuma abubuwan da kasarsa da ma Afirka ke jira daga wannan ziyara inda yake cewa:

"Na farko dai ina mai cike da farin ciki da zuwa nan Jamus, domin bayan samun mulkin kai yau shekaru kusan 60 sai a wannan karon ne wani shugaban Chadi ya kawo ziyarar aiki a kasar Jamus don haka wannan abun alfahari ne a gare ni. Duk da cewa tare da Jamus muna da huldodi ta hanyar Tarayyar Turai, sannan kuma muna da huldodi na tsakanin kasa da kasa ta hanyar hukumar hadin kan taimakon fasaha ta GTZ da kuma bankin KfW. Sannan a fannin tattalin arziki, za mu gayyaci manyan 'yan kasuwa na Jamus su zo domin zuba jari a Chadi. Ta haka ne ma na zo da shugaban cibiyar kasuwanci na Chadi, da kuma manyan 'yan kasuwa domin su tattauna da takwarorinsu na Jamus."


Berlin Merkel trifft Tschads Präsident Idriss Deby Itno (picture-alliance/AP Photo/M. Schreiber)

Idriss Deby da Angela Merkel a taron manema labarai a Berlin

A fannin yaki da ta'addanci musamman ma na 'yan kungiyar Boko Haram da kasar ta Chadi ke taka rawar gani, shugaba Deby ya yaba da yadda kasashen da ke kewayen tafkin Chadi gami da kasar Benin ke kokari na ganin an samu dawo da zaman lafiya a tsakanin wadannan kasashe.

"Na farko dai mun tattauna a kan batutuwan da suka shafi kwararar bakin haure, da batun safarar miyagun kwayoyi a yankin Sahel, da batun tashe-tashen hankula da ake fuskanta a kasashen Afirka, da kuma hanyoyin magance su, sannan da batun halin da 'yan gudun hijira ke ciki. Kuma dukannin wadannan matsaloli ne da ke haifar da babban cikas a rayuwar 'yan gudun hijra da kuma al'ummomin kasashen da 'yan gudun hijirar suke. Duk wadannan na daga cikin batutuwan da muka tattauna da Shugabar gwamnatin Jamus. A fannin Boko Haram sai a ce kasashen da ke kewaye da tafkin Chadi sun taka rawar gani musamman ma bayan isowar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kan mulki. Sai dai ana iya cewa matsalolin da 'yan kungiyar suka haddasa na tsawon shekaru hudu sun shafi al'ummomi kai tsaye."


Berlin Demonstration Anti Idriss Deby (Aabdelkerim Yacoub Koundougoum)

Zanga-zangar kin lamirin Idriss Deby lokacin ziyararsa a Berlin

Shugaban na Chadi kuma shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka Idriss Deby Itno ya yi kira ga kasashen Turai da sauran masu fada a ji a duniya da su taimaka a shawo kan matsalar da ake fuskanta a yankin Sahel ta dalilin wargajewar kasar Libiya, inda yake cewa:

"Hakan sakamako ne na matakan da suka dauka ba tare da shawara da kasashe makwabtan Libiya, ko kuma Tarayyar Afirka ba. Kaman dai a lokacin mulkin mallaka kawai a zo a hargitsa kasa guda ana ji ana gani. Sannan kuma ba tare da sun shawarcemu ba suna tsammanin za su iya shawo kan matsalar Libiya. Mu dai a shirye muke mu kama wa Martin Kobler mai shiga tsakanin na Majalisar Dinkin Duniya kan batun Libiya dan ganin an samu mafita, kuma ala tilas sai an bai wa 'yan kasar Libiya damar tattaunawa da junansu."

Sai dai kuma a daura da wannan ziyara, 'yan kasar Chadi mazauna nan Jamus sun yi cincirindo domin nuna adawarsu ga wannan ziyara ta shugaba Deby inda suka ce bai kamata ba a daidai wannan lokaci da ake fama da tashe-tashen hankula na cikin gida a kasar ta Chadi, sabili da gurbataccen zabe da shugaban mai ci ya shirya wanda har yanzu 'yan adawar kasar da ma kungiyoyin farar hula ba su aminta da shi ba. Hakan a cewarsu, na a matsayin wani mataki na nuna amincewa da wannan dan kama karya a fagen siyasar duniya.

Sauti da bidiyo akan labarin