Jamus tayi suka ga Idris Derby na kasar Tchad | Labarai | DW | 13.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus tayi suka ga Idris Derby na kasar Tchad

Ministar maaikatar raya kasashen ketare ta nan Jamus,Heide Marie WiekzorekZeul tayi Allah wadai da babban murya wani mataki da shugaban kasar Tchadi Idris Derby ya dauka na sanya hannu akan dokar da ta shafi yadda zaa kashe kudaden da Tchadin take samu daga cinikin man fetur,tace ba zai yiwu Tchadin taki anfani da kudin wajen taimakawa talakawan kasar ba.

Ta kara da cewa sakamakon wannan mataki ana tsoron cewa mafi yawab kudaden ana iya anfani da su wajen aikin soja da kuma toshe gibin da ake samu a kasafin kudin kasar,wadda yake samuwa daga rashin iya tafiyar da aikin gwamnati.

A bisa maida martani,maaikatar kula da raya kasashen ketare ta jamus ta nuna goyon bayanta da dakatar da duk wani taimako da bankin duniya yace zai yiwa Tchadi,ta kuma dakatar da shawarwari da suka shafi hadin kan taimakon raya kasa tsakanin gwamnatin Jamus da Tchadi kuma zata hada kai da gwamnatocin wasu kasashe domin nazarin matakan da zaa dauka na ladabtar da Tchadi.