Jamus ta nemi sakin Jamusawa a Turkiyya | Siyasa | DW | 29.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jamus ta nemi sakin Jamusawa a Turkiyya

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta nemi da Turkiyya da ta sako Jamusawan da take ci gaba da tsarewa a kasarta, inda ta ce babu wasu cikokun hujjoji na tsare su.

Deutschland Wahlkampf CDU Kanzlerin Merkel in Bitterfeld-Wolfen (picture-alliance/dpa/H. Schmidt)

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel lokacin yakin neman zabe

Daga cikin muhimman batutuwan da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi magana kansu a ganawarta da ‘yan jaridu a wannan Talatar, akwai batun dubban ‘yan gudun hijira da suka shigo kasar shekaru biyun da suka gabata. Merkel din da ke magana kasa da wata guda da babban zaben kasar da za a yi na ranar 24 ga watan Satumba, ta kuma ce an tsara matakan hana sake aukuwar kwararar ‘yan gudun hijira zuwa Jamus a nan gaba.

Yayin da tabo batu mai alaka da kasar Turkiyya, Merkel din ta amince da raunin dangantaka da ke tsakanin kasashen biyu, inda kuma ta bukaci Turkiyyar da ta sako Jamusawan da take ci gaba da tsare su, bayan yunkurin kifar da gwamnatin kasar da bai yi nasara ba, tana mai bayyana ci gaba da tsare sun a matsayin maras hujja.

Sanyin dangantaka tsakanin Jamus da Turkiyya

Deutschland PK Merkel (picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka)

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta na hira da 'yan jaridu

"A halin da ake ciki, akwai abin da ke faruwa a Turkiyya, watau na ci gaba da tsare wasu Jamusawa, wanda nake ganin tana yin haka ba tare da wata kwakkwarar hujja ba. Abin da zan ce dai, ganin yadda Jamus ke dauke da Turkawa miliyan uku, abin da za mu bukata shi ne dangantaka ta kwarai da ke tafiya da bin dokoki. Abin dai da muke bukata a takaice shi ne na sakin ‘yan kasarmu da ke tsare a kasar a halin yanzun."

Batun bincike kan iyakokin kasashen Turai da ke zirga-zirga tsakanin juna dai batu ne da kasashen suka bashi muhimmanci musamman lokacin da suka fuskanci kwararar 'yan gudun hijira, sai dai hukumar Tarayyar Turai ta kawo tsaikon da Merkel ta ce akwai bukatar sake tsari.

 

Sauti da bidiyo akan labarin