Jamus ta bukaci Girka ta fara sauye-sauye. | Labarai | DW | 21.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta bukaci Girka ta fara sauye-sauye.

Tarayyar Jamus ta bayyana fatan ganin mahukuntan kasar Girka sun fara aiwatar da kudurorin da aka cimma kan batun sabbin sauye- sauye na ceto halin da tattalin arzikin kasar Girka.

Mai magana da yawun shugabar gwamnatin Jamus Steffen Seibert a yayin da yake ganawa da manema labarai ya ce tsarin jadawalin shirin an amince da shine ne a tsakanin tarayyar Turai da kasar Girka kuma shirin zai dauki shekaru uku ana aiwatar dashi.

Bugu da kari ya ce gwamnatin Tarayyar Jamus kamar sauran gwamnatocin kasashen kungiyar EU na matukar sauraron fara aiwatar da sauye- sauyen a karkashin yarjejeniyar da aka cimma daga bangaran kasar Girka.

Kazalika kasar Jamus tayi gargadin cewar duk wani nawa da aka samu kan aiwatar da shirin to hakan na iya janyo kin biyan kudaden tallafi cikin hanzari.