1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Rasha ta sansanta da Ukraine

December 11, 2018

Shugabar gwamnatin Jamus ta bukaci Rasha da Ukraine su daidaita rikicin da ke tsakninsu don kwantar samun kwanciyar hankali.

https://p.dw.com/p/39phw
Bundeskanzlerin Angela Merkel telefoniert
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Schreiber

Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta bukaci gwamnatin kasar Rasha da ta hanzarta sakin jiragen ruwan kasar Ukraine 24 ne da ta kama cikin watan jiya.

Angela Merkel ta bukaci hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da ta yi da Shugaba Putin na Rasha a jiya Litinin, kamar yadda mai magana da yawunta Steffen Seibert ya sanar.

Tun da fari dai sai da shugabar gwamnatin ta Jamus Merkel ta shaida wa Shugaba Putin cewar kamata ya yi Rasha da Ukraine su mayar da wuka kube a takaddamar da suke samu tsakanin juna.

Ta kuma bukaci kasashen biyu su samar da hanyoyin shiga a tsakanin juna ba tare da tayar da jijiyoyin wuya ba, tare da jaddada cewar babu amfanin amfani da karfin soji.