Jamus na nazarin yiwuwar tura dakarunta zuwa Kongo | Labarai | DW | 15.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus na nazarin yiwuwar tura dakarunta zuwa Kongo

Gwamnatin tarayyar Jamus na nazarin yiwuwar ba da gudummawar sojojin leman kasar ga wata rundunar da Kungiyar Tarayyar Turai zata tura kasar JDK. Rahotanni daga ma´aikatar tsaro sun ce kungiyar EU na shirin tura dakaru kimanin dubu daya da 500 don tabbatar da tsaro a lokacin zaben gama gari da zai gudana a Kongo a cikin watan afrilu. Ma´aikatar ta ce za´a tura rundunar ce bisa rokon MDD. To sai dai har yanzu gwamnati ba ta yanke shawara akan wannan batu ba. ´Yan adawa musamman na bangaren jam´iyar Free Democrat na son gwamnati ta yi watsi da wannan shawara bisa hujjar cewa tuni sojojin Jamus suka shagala wajen aikin wanzar da zaman lafiya a Afghanistan, yankin Balkans da kuma a wasu kasashen nahiyar Afirka.