1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar neman kare muhalli

Ramatu Garba Baba
October 7, 2019

Daruruwan masu fafutukar kare muhalli ne suka soma gudanar da wata zanga-zanga ta mako guda da zummar tilastawa gwamnati daukar kwararan matakai na kare muhalli.

https://p.dw.com/p/3QqbJ
Deutschland Berlin | Klimaprotest Extinction Rebellion
Hoto: picture-alliance/dpa/C. Koall

Kamar sauran kasashen nahiyar Turai, Berlin babban kasar Jamus ya fuskanci cunkoson ababen hawa bayan da masu zanga-zanga suka mamaye dandalin Tiergarten da ke tsakiyar birnin don jan hankulan gwamnati kan daukar matakin kare muhalli daga barazanar Sauyin yanayi.

Duk da tsananin yanayi na sanyi, bai hana jama'a fitowa ba. A ranar Laraba mai zuwa ne, ake sa ran Shugabar gwamnati Angela Merkel za ta sanya hannu kan wani kuduri da aka shata na samar da mafita, sai dai kafin a sanya hannun ma, kudurin ya soma shan suka. Daya daga cikin batutuwan da ya kunsa da bai yi wa jama'a dadi ba, shi ne karin kudin makamashin da ake son yi.