Ko jam'iyyar AfD na kara karfi a Jamus?
September 15, 2025
Sakamakon zaben ya nunar da cewa, jam'iyyar The Greens ta fuskanci koma-baya sosai idan aka kwatanta da shekaru biyar da suka gabata. Jam'iyyar AfD da ke kyamar baki ta samu karuwar kuri'u, lamarin da ya ba ta damar zama jam'iyya ta uku mafi karfi a jihar da ke yammcin Jamus.
Jam'iyyar CDU da ke da ra'yin rikau, ta ci gaba da kasancewa a kan gaba da yawan kuri'u a jihar North Rhine-Westphalia da ke zama mahaifar shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz. Duk da cewa ta lashe sama da kaso 34 na kuri'un da aka kada a jihar da ta fi yawan al'umma, amma koma-bayan da ta samu in aka kwatanta da zaben kananan hukumomi na 2020 bai taka kara ya karya ba.
Shin mai nasarar CDU a wannan jiha ke nufi?
Gwamnan jihar North Rhine-Westphalia Hendrik Wüst da ya kasance dan jam'iyyar CDU, ya danganta nasarar da suka samu da aikin da suke yi wajen magance matsalolin da ke ci wa al'umma tuwo a kwarya. Ya ce: "Wannan kyakkyawan sakamakon zaben, kuri'a ce ta siyasar tsaka-tsaki mai neman mafita ga matsaloli."
Karin Bayani:AfD na zawarcin matasa gabanin zabe a Jamus
Jam'iyya ta biyu da ta samu ci-gaba a zaben kananan hukumomin North Rhine-Westphalia, ita AfD ta masu tsattsauran ra'ayin kishin kasa da kyamar baki. Hasali ma ta ninka kuri'un da ta samu a zaben 2020, inda ta tashi daga kaso biyar zuwa kaso 15 cikin 100. Ko da yake AfD ta kafu a jihohin gabashin Jamus, amma wannan shi ne karon farko da ta samu tarin kuri'u a jihar da ta kunshi kaso daya bisa hudu na al'ummar Jamus.
Ko Jamusawa sun fara rungumar AfD?
'Yar majalisar dokokin jihar NRW ta Gelsenkirchen 'yar AfD Enxhi Seli-Zacharias ta ce, sannu a hankali sun fara samun karbuwa a jihar. A cewarta: "Ga jam'iyyar AfD abu daya da ya fito shi ne, mun karfafa yawan masu kada mana kuri'a.
Sai dai kuri'un da jam'iyyar SPD da ke kawance a gwamnatin tarayya ta samu sun ragu sosai, musamman in aka yi la'akri da cewar jihar North Rheine-Westepahalia ce tungar tsarin matsakaicin ra'yin gurguzu a Jamus. Ita dai jam'iyyar ta tsohon shugaban gwamnati Olaf Scholz ta tashi da sama da kaso 22 cikin 100 na kuri'un da aka kada, sabanin kaso 24 cikin 100 da ta samu shekaru biyar din da suka gabata.
Amma daya daga cikin shugabanin SPD Bärbel Bas ta danganta sakamakon da suka samu da tuntuben dadin gushi, a cewarta: "Gaskiya ne cewa ba za mu yi nasarar ja wa koma-bayan da muke fuskanta birki ba, amma kuma ba gaskiya ba ne cewar jam'iyyar SPD na fuskantar wani bala'i."
Karin Bayani: CDU da SPD za su koma tattaunawa don kafa gwamnati a Jamus
Ita kuwa jam'iyyar The Greens ta kasance wacce ta fi ja-baya a zaben kananan hukumomi na jihar North Rhine-Westphalia, inda ta samu sama da kaso takwas cikin 100 na kuri'un da aka kada, alhali ta tashi da sama da kaso 11 ne a zaben 2020. Duk da cewa sakamakon ya kona wa magoya bayanta zuciya, amma daya daga cikin shugaban jam'iyyar Felix Banaszak ya ce sakamakon ya yi kan-kan-kan da karbuwar da suka samu a matsayin tarayya: "Sakamakon ya yi kusan kama da wanda muka samu a zaben tarayya."
Yadda za a zabi magajin gari
A ranar 28 ga wannan wata na Satumbar 2025 ne za a gudanar da zagaye na biyu na zaben kananan hukumomi a North Rhine-Westphalia, domin tantance magajin gari a tsakanin wadanda suka zo na daya da na biyu.