1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Zaben hukumomi ko gwajin dafi ga siyasar Jamus?

Christoph Hasselbach Mouhamadou Awal Balarabe
September 13, 2025

Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nunar da cewar jam'iyyar SPD na iya samun komabaya a zaben kananan hukumomi na jihar North Rhine-Westphaliada take da karfi, yayin da jam'iyyar AfD mai kyamar baki za ta iya samun ci-gaba.

https://p.dw.com/p/50Qjr
Yawancin jam'iyyun Jamus sun tsayar da 'yan takara a zaben kananan hukumomin jihar North Rhine-Westphalia
Yawancin jam'iyyun Jamus sun tsayar da 'yan takara a zaben kananan hukumomin jihar North Rhine-WestphaliaHoto: Revierfoto/dpa/picture alliance

Ya kamata ya zama zaben kananan hukumomi ne kawai a jihar da ta fi yawan al'umma a Jamus. Amma ya kasance zaben farko a kasar tun bayan kafa gwamnatin hadaka da ta kunshi jam'iyyun CDU/CSU masu ra'ayin rikau da SPD da ke da matsakaicin ra'ayin gurguzu. Saboda haka ne Oliver Lembcke, masanin kimiyyar siyasa a jami'ar Bochum ya danganta da shi da zaben gwajin dafi ga jam'iyyun da ke rike da madafun iko a matsayin kasa baki daya.

Karin bayani: Merz ka iya samun kalubale a siyasar ketare

Sannan zaben na da mahimmanci saboda North Rhine-Westphalia ce jihar da ke da yawan jama'a kusan miliyan 18. Hasali ma, bambance-bambancen da ake fuskanta a fannin tattalin arziki da zamantakewa a jihar sun zama mizani ga halin da Jamus ce ciki. A hanzu haka, kusan kashi daya cikin hudu na mazauna jihar NRW kamar sauran jihohin Jamus suna da asalin da ketare.


 Abubuwan da ke ci wa al'umma tuwo a kwarya

Rashin gyara makaratu na cikin matsalolin da ke ci wa mazauna jihar North Rhine-Westphalia tuwo a kwarya
Rashin gyara makaratu na cikin matsalolin da ke ci wa mazauna jihar North Rhine-Westphalia tuwo a kwaryaHoto: Guido Kirchner/dpa/picture alliance

Ana daukar jihar North Rhine-Westphalia musamman yankin Ruhr, a matsayin "tungar tsarin gudanarwa na matsakaicin ra'ayin gurguzu". Sannan shugabar gwamnatin Jamus Friedrich Merz na jam'iyyar CDU ya fito ne daga jihar. Don haka dukkanin bangarorin biyu da ke tafiyar da gwamnatin tarayya na dokin jiran sakamakon zaben na kananan hukumomi.

Karin bayani: Tasirin zaben Brandenburg a siyasar tarayyar Jamus

Sai dai mutane da yawa a jihar North Rhine-Westphalia ba su gamsu da yadda ake tafiyar da kananan hukumominsu ba, musamman ma dangane da ababen more rayuwa, in ji Oliver Lembcke, masanin kimiyyar siyasa a jami'ar Bochum: 

Ya ce: "Hanyoyi, gadoji, sufuri, makarantu, na daga cikin abubuwan da ke mutane ke saurin korafi a kai, suna jin cewa 'yan siyasa ba sa kula da su. Muna ganin cewa batutuwa masu mahimmanci na siyasar kasa na taka rawa, kamar hijira, kamar yawan bakin haure." 

AfD ba za ta samu magajin gari ba duk da nasarorin da za ta samu


Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nunar da cewar jam'iyyar SPD na iya asarar kuri'u masu tarin yawa a zaben kananan hukukokin NRW, musamman a garuruwan Gelsenkirchen da Duisburg. Yayin da a bangarenta, jam'iyyar AfD mai tsattsauran ra'ayin siyasa na iya samun karfi a gundumomin.

Jam'iyyar AfD na mai da hankali kan matsalar bakin haure, duk da cewa ba hurumin kananan hukumomi ba ne
Jam'iyyar AfD na mai da hankali kan matsalar bakin haure, duk da cewa ba hurumin kananan hukumomi ba neHoto: Caroline Seidel-Dißmann/dpa/picture alliance

A zabukan kananan hukumomi da suka gudana shekaru biyar da suka gabata, jam'iyyar AfD ta samu kusan kashi 5% ne kawai; amma a wannan karon, an yi hasashen cewar za ta iya ninka kuri'unsu sau uku.

Karin bayani: AfD na zawarcin matasa gabanin zabe a Jamus

Amma masanin siyasa Oliver Lembcke, ya yi imanin cewar ba za a samu magajin gari dan AfD ba a zabukan kananan hukumomin NRW: Ya ce: "A lokacin zaben shugabannin kananan hukumomi (inda ake zaben 'yan takara kai tsaye), kawancen za su kullu saboda sauran jam'iyyun za su amince da dan takarar da ya fi dacewa domin nuna masa goyon bayansu, ta haka ne za su hana jam'iyyar AfD samun magajin gari."

Rashin gamsuwa da kamun ludayin gwamnatin tarayya


Mummunan yanayi da manyan jam'iyyun ke ciki a North Rhine-Westphalia ba ya rasa nasaba da rashin gamsuwa da ayyukan gwamnatin tarayya, inda wani sabon kididdigar jin ra'ayin jama'a da ARD ta gudanar ke nuna cewar kashi 22%i ne kawai suka gamsu da ayyukan gwamnatin tarayya a fannoni daban-daban a fannin tattalin arziki, da manufofin ketare, da manufofin haraji da kasafin kudi.