Jamus: An yi tir da masu boren adawa da matakan kariya na Covid-19 | Siyasa | DW | 31.08.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jamus: An yi tir da masu boren adawa da matakan kariya na Covid-19

Masu tsauttsauran ra'ayin kyamar baki a Jamus sun yi amfani da zanga-zangar da wajen danna ki majalisar dokoki amma jami'an tsaro sun taka musu birki.

'Yan siyasar Jamus da jami'an tsaro da ma sauran jama'a na ci gaba da mayar da martani kan zanga-zangar da masu adawa da matakan kariya na yaki da corona suka yi a gaban ginin nan na Reichstag da majalisar dokokin kasar ke da mazauninta.

Shi dai wannan ginin na Reichstag da aka samar da shi a karshen karni na 19, a zamanin Sarki Kaiser Wilhelm II na da muhimmanci ga siyasar kasar kasancewar abubuwa da dama na tarihi da kuma dunkulewar kasar waje guda don kuwa a cikinsa ne a shekarar 1918 aka ayyana kasar a matsayin tarayya a karon farko. To sai dai a shekarar 1933 'yan Nazi sun banka masa wuta wani yunkuri na wargaza tarayyar kasar amma kuma sojin Sobiet sun yi amfani da shi a 30 ga watan Afrilun shekarar 1945 a matsayin wajen da suka daga tutar da ke alamta samun nasara kan mulkin 'yan Nazi.

Kutsen da aka yi wa ginin a ranar Asabar din da ta gabata ta sanya nuna damuwa daga ciki da wajen kasar, musamman ma dai ga masu rike da madafun iko da kuma wanda ke kyamar masu tsaurin ra'ayi da tsarin tafiyarsu ke kama da ta 'yan Nazi.

Steinmeier ya gana da 'yan sandan da suka katse hanzarin wadanda suka yi yunkurin shiga ginin Reichstag

Steinmeier ya gana da 'yan sandan da suka katse hanzarin wadanda suka yi yunkurin shiga ginin Reichstag

Shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier na daga cikin na sahun gaba a wadanda suka fara tofa albarkacin bakinsu kan wannan batu, wanda ya kira hari kan tsarin dimukuradiyyar kasar musamman ma dai baza tutar kungiyar nan ta 'yan Reichbürger da kurarsu ta yi kuka wajen tsaurin ra'ayi na kyamar baki.

"Sanya tutocin 'yan Reichbürger ciki kuwa har da wadanda ke alamta yaki a mashigar majalisar dokokinmu da ka zaba kan tafarkin dimukuradiyya abin bakin ciki da Allah wadai ne idan muka dubi tarihin wajen. Ko da wasa ba za mu amince masu kyamar dimukuradiyya su lalata sunan Jamus a gaban ginin maljalisar dokokin kasarmu ba."

Da yake nasa tsokacin kan wannan lamari, Steffen Seibert da ke magana da yawun shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel cewa ya yi abin da ya faru gaban zauren majalisar dokokin kasar a karshen mako abin takaici ne da wasu marasa kan gado suka yi. Kuma a cewarsa a fakaice sun yi amfani da damar da suke da ita ta yin zanga-zanga wajen yin aika-aikar da suka yi.

"A karshen mako mun ga misali na yin karan tsaye ga amfani da 'yanci da kuma damar da dan kasa ke da ita na yin zanga-zanga. Damar da kowa ke da ita ta nuna rashin amincewarsa kan wani abu musamman a lokacin annoba irin na corona na da kyau amma kuma amfani da ita ta hanyar da ba ta dace ba abin bakin ciki ne. Irin abin da ya wakana a ginin Reichstag abu ne da ba za mu lamunta ba. Yanzu kam an yi walkiya mun ga wadanda ke kyamar tsarin dimukurayyar da kasarmu ke kai."

Ministan cikin gida Horst Seehorfer na daga cikin 'yan siyasa a Jamus da suka yi tir da masu boren

Ministan cikin gida Horst Seehorfer na daga cikin 'yan siyasa a Jamus da suka yi tir da masu boren

Shi ma dai ministan cikin gidan Jamus din Horst Seehofer nuna damuwarsa ya yi kan yadda masu tsaurin ra'ayin suka yi amfani da wannan zanga-zanga ta masu adawa da matakan kariya na corona din, don shiga ginin da nufin aiwatar da wasu manufofinsu da suka saba da tafarkin da kasar ke kai, yayin da ministan harkokin waje Heiko Maas a wani sako da ya wallafa ta shafinsa na Twitter yake cewar wannan abu da aka aikata abin kunya ne musamman ma tutocin da aka rika bazawa a wajen na 'yan kungiyar nan ta Reichbürger ta masu kyamar baki a gaban zauran majalisar dokokin kasar.

Tuni dai masu sharhi kan lamuran da ke kai su komo a fagen siyasar Jamus din su ma suka fara tofa albarkacin baki kan wannan batu da ya rikide daga zanga-zangar corona zuwa afka wa ginin majalisar dokokin kasar da masu tsaurin ra'ayi suka yi. Katharina Nocun guda ce daga cikin masharhanta da suka magantu inda ta ce irin kungiyoyin da suka hadu a wajen abin tayar da hankali ne matuka, domin kuwa a cewarta wadanda suka shirya zanga-zangar ba su nesanta kansu daga kungiyoyi irin na 'yan Reichbürger ba, hasali ma sun yi ta nanata cewar da su da irin wadannan kungiyoyi na da abokiyar gaba guda ne wato gwamnatin kasar. Yanzu haka dai da ma a ciki da wajen Jamus na zuba idanu don ganin irin mataki na gaba da hukumomi za su dauka kan irin wadannan kungiyoyi da ma irin hukuncin da zai hau kan wanda aka kama da zargin ta da wannan tashin-tashina da ta girgiza gwamnati.

Sauti da bidiyo akan labarin