Israela ta fada cikin rudani na siyasa
May 2, 2007Faraministan Israela Ehud Olmert yayi watsi da kiraye kirayen da yan jam´iyyar sa ta Kadima keyi, na murabus daga mukamin sa.
Bukatar yin murabus din dai ta biyo bayan samun hannun faraministan ne dumu dumu da nuna rashin adalci, a lokacin yakin da kasar ta gwabza da kasar Libanon.
An gano haka ne kuwa a yayin da wani kwamiti da aka dorawa alhakin bincike kann yakin ya fiddo da rahotan sane, a ranar litinin din data gabata.
Ci gaba da kiraye kirayen murabus din Faraministan dai ya biyo bayan murabus din da ministar harkokin wajen kasar , wato Tzipi Livni tayi ne a jiya talata.
A kuri´ar neman jin ra´ayin jama´a da aka gudanar an gano cewa kashi 65 na mutanen kasar na bukatar faraministan yin murabus daga mukamin nasa.
Mutane dai a kalla dubu daya da dari uku da sittin ne suka rasa rayukan su daga bangarorin biyu, a lokacin yakin da Israelan ta gwabza da kasar ta Libanon.