Hukumar IAEA ta nanata kira ga Iran | Labarai | DW | 15.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar IAEA ta nanata kira ga Iran

Shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta majalisar ɗinkin duniya Mohammed el-Baradei ya yi kira ga kasar Iran ta dakatar da bunƙasa makamashin Uranium domin bada dama ta sasanta taƙaddamar wadda manyan ƙasashe na duniya ke buƙatar Tehran ta dakatar da shi ɗungurungum. El-baradei yace ƙin amincewar Iran na dakatar da shin nukiliyar tamkar fito na fito ne take yi da kwamitin tsaro na majalisar ɗinkin duniya. To sai dai yace tunanin yin amfani da ƙarfin soji akan Iran zai kasance rashin hankali. Da yake jawabi a ƙarshen taron hukumar ta IAEA a game da shirin nukiliyar, el-Baradei yace Iran na cigaba da bunƙasa fasahar makamashin.