1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Coronavirus: Mai zai faru a 2022?

Hasselbach, Christoph SB/LMJ
December 20, 2021

Sabuwar gwamantain Jamus, na son bai wa al'umma tabbaci a siyasance. Sai dai matsalolin siyasa a duniya da kuma annobar coronavirus, na sa zuciyoyi a damuwa.

https://p.dw.com/p/44a4Q
Belgien Gipfel Bundespräsident Olaf Scholz
Corona ka iya zama babban kalubale ga sabon shugaban gwamnatin Jamus Olaf ScholzHoto: Alexey Vitvitsky/Sputnik/dpa/picture alliance

A Jamus lokacin shiga sabuwar shekarar da ta gabata annobar cutar coronavirus da duniya ta samu kanta ke zama babban abin da ya dauki hankali a kasar. Yayin da ake shirin shiga sabuwar shekara ta 2022, har yanzu annobar coronavirus ta kasance wadda ke daukar hankali a ciki da wajen kasar. A wannan lokaci dangane da batun tabbatar da ganin kowa ya yi rigakafin cutar, domin kaucewa matsalolin da cutar ke haifarwa. An dai ba da miliyoyin allurar riga-kafin cutar ta coronavirus, amma daga bisani an kuma samu karuwar masu kamuwa da cutar a tsakiyar watan jiya na Nuwamba.

Karin Bayani: Al'umma na shakku kan rigakafi a Jamus

Wannan ya saka cibiyar kula da cutuka masu yaduwa ta Jamus, yin gargadin irin kasadar da ake ciki a cewar shugaban cibiyar Lothar Wieler. Domin tabbatar da ganin kusan daukacin mutanen Jamus sun yi riga-kafin, gwamnati ta karfafa matakai kan hana wadanda ba su yi allurar ba shiga wuraren da ba tilas ba kamar shagunan da sayar da kaya da makamantansu sai dai idan wanda bai dade daga warkewa daga cutar ba.

Sabuwar gwamnati karkashin Olaf Scholz da sauran da ke cikin kawance, na son jaddada dokokin da aka gindaya karkashin gwamnatin da ta gabata ta tsohuwar shugabar gwamnati Angela Merkel. Sabon shugaban gwamnatin Scholz ya ce lamarin na bukatar hadin kai tsakanin kasashe domin dakile annobar. Sai dai akwai rarrabuwar kai tsakanin al'umma kan matakan da suka dace na dakile annobar ta coronavirus, musamman kan tilasta mutanen su yi riga-kafi.

Karin Bayani:Angela Merkel da rayuwa bayan gama mulki

Jam'iyyun SPD da The Greens mai kare muhalli gami da FDP mai neman sakin mara ga harkokin kasuwanci da suka kafa gwamnatin hadaka a Jamus din, suna da fata kan samun goyon bayan da ya dace kan hanyoyin dakile cutar. Jamus ta nunar da cewa yayin da ake neman hanyoyin magance annobar coronavirus, ba za a manta da batutuwan tsaro da barazanar da Rasha ke yi wa Ukraine ba, ko kuma yadda Chaina take kara angizo a yankin tekun Chaina. Abin da sabon shugaban gwamnatin ta Jamus Olaf Scholz ya ce abubuwan da ke faruwa a duniya suna da tasiri ga kasar kan tsaro. Jamus tana fata ta nuna tasirinta, lokacin taron gaggan kasashe masu karfin tattalin arziki na G7 a shekara mai zuwa ta 2022.