1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron shugabannin G7 ido na ganin ido

Mohammad Nasiru Awal LMJ
June 11, 2021

A wannan Jumma'a shugabannin kasashe masu karfin tattalin arziki na kungiyar G7, sun bude taron kolinsu na ido na ganin ido a karon farko cikin kusan shekaru biyu.

https://p.dw.com/p/3umM7
G7-Gipfel in St Ives 2021
Shugabannin kasashen kungiyar G7 na yin taro ido na ganin idoHoto: Koji Ito/Yomiuri Shimbun/picture alliance

Kasashen masu tagomashin tattalin arziki a duniya da suka hadar da Birtaniya da Kanada da Faransa da Jamus da Italiya da Japan da kuma Amirka, sun ce hada karfi waje guda shi ne babbar mafita da duniya ke da ita don farfado wa daga annobar cutar corona da ta kassara fannin kiwon lafiya da kuma magance matsalar sauyin yanayi. A lokacin da yake maraba da takwarorinsa a gun taron da ke yankin shakatawa na Carbis Bay da ke Corwall a Kudu maso Yammacin Ingila, firaministan Birtaniya Boris Johnson ya bude zango farko na taron kolin da shugabannin suka ba da tazara tsakaninsu amma ba su saka takunkumi ba.

Karin Bayani: Gobarar Amazon ta mamaye taron G7

Shugaban Amirka Joe Biden wanda wannan shi ne taron kolin farko na kungiyar G7 da ya halarta tun bayan darewarsa kan kujerar shugabancin Amirka a farkon watan Janairun wannan shekara, kuma ya dawo daga rakiyar manufar tsohon shugaban Amirka Donald Trump ta mayar da wasu kasashe saniyar ware yana mai aike sakon sulhu na G7 ga kungiyar NATO da kasashen Chaina da Rasha, inda a mako mai zuwa zai kai ziyara. Biden ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa yana sa ran karfafa kudurin da suka dauka na inganta dangantaka da kasashen duniya tare da yin aiki da kawayen Amirka, domin gina abin da ya kira tattalin arzikin duniya da zai tafi da kowa.
A jawabinta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta jaddada kudurin sake farfado da tattalin arzikin duniya, ta kuma yi kira da a hada karfi da karfe a yakin da ake da sauyin yanayi da kuma tallafa wa kasashe matalauta samun alluran riga-kafin corona: "Ina farin cikin shugaban Amirka yana nan tare da mu. Haduwa da shi yau muhimmin abu ne gare ni domin yana goyon bayan tafiya da kowa a batutuwan kasa da kasa, abin da muka rasa a shekarun baya-bayan nan. A lokaci daya muna son mu yi aiki da kowa a duniya musamman a kan batutu kare muhalli, ba kuma za mu kai ga tudun dafa wa ba sai mun hada da kasar Chaina."

Ost-Ministerpräsidentenkonferenz | Bundeskanzlerin Angela Merkel (CDU)
Shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: Annegret Hilse//Reuters/Pool/dpa/picture alliance

Karin Bayani:An soma taron ƙungiyar ƙasashen G7

Shugabar gwamnatin ta Jamus ta yi fata taron zai samar da sakamako na a zo a gani ba kawai ga kasashe masu arziki ba, har ma ga wadanda kawo yanzu ba su samu damar yin allura riga-kafi ba, musamman a kasashen Afirka da wasu sassan duniya. Ana sa rai a karshen taron shugabannin za su alkawarta ba da alluran riga-kafin cutar corona miliyan 1000 ga kasashe matalauta, a wani mataki na nuna tafiya da kowa a yakin da ake da annobar. A daura da taron masu rajin kare muhalli sun yi zanga-zangar kira ga shugabannin na G7 da su fito da kwararan matakan magance matsalar sauyin yanayi.