1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar G7: Hankali ya karkata kan batutuwa da dama

Gazali Abdou Tasawa AMA
August 26, 2019

Taron kungiyar G7 ta kasashe mafi karfin tattalin arziki a duniya da ya gudana ya kawo karshe tare da daukar matakai a kan batutuwa da dama da suka hada da matsalar tsaro a yankin Sahel da kuma ta gobarar a dajin Amazon

https://p.dw.com/p/3OWFc
Shugabannin kasashen kungiyar G7 a yayin da suke ganawa
Shugabannin kasashen kungiyar G7 a yayin da suke ganawa Hoto: Getty Images/AFP/P. Wojazer

Dangane da batun gobarar da ke ci gaba da yaduwa a dajin na Amazon taron kungiyar ta G7 ya dauki matakin bayar da tallafin gaggawa na kudi sama da miliyan 20 na dalar Amirka domin dauko hayar karin jiragen kashen gobara dan ganin an murkusheta wutar. 

Babban Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya sake yin kira ga kasashen duniya da su kara himma wajen ganin an ceto dajin na Amazon mai fadin murabbadin kilomita miliyan biyar da rabi da kuma ke da tasirin wajen samar da daidato ga muhallin duniya.

G7-Gipfel in Frankreich Macron and Guterres
Hoto: picture-alliance/abaca/S. Ortola

Wata hukuma da ke sa ido kan yanayin gobarar da ke ci gaba yanzu haka da ci a dajin na Amazon ta bayyana cewa daga Asabar zuwa Lahadi kadai wutar ta tashi a wurare sama da dubu uku, a dajin wanda ya kunshi nau'o'in tsirra sama da budu 30 da tsuntsaye da nau'o'i 1.500 da namun daji da kifaye sama da 2.500.

Yankin Sahel ya ja hankalin taron G7

Shugaban kasar Burkina Faso kuma shugaban kungiyar G5 Sahel a yayin taron G7
Shugaban kasar Burkina Faso kuma shugaban kungiyar G5 Sahel a yayin taron G7Hoto: Getty Images/AFP/I. Langsdon

Batun matsalar tsaro a yankin Sahel na daga cikin jerin batutuwan da taron na G7 ya tattauna a kai inda da yake jawabi a wurin taron Shugaba Roch Marc Christian Kabore na kasar Burkina Faso kuma shugaban kungiyar G5 Sahel, ya yi kira ga kasashen duniya da su gaggauta daukar matakan shawo kan rikicin kasar Libiya wanda ya ce ta haka ne kadai za a iya dakile matsalar ta'addancin da ta yi kaka gida a yankin na Sahel.

Yunkurin G7 na kashe wutar rikicin Iran

Tattaunawa tsakanin hukumomin kasar Iran a yayin taron G7
Tattaunawa tsakanin hukumomin kasar Iran a yayin taron G7Hoto: picture-alliance/AP Photo/Twitter Javad Zarif

Wani batun na daban da ya dauki hankalin taron na G7 shi ne rikicin nukiliyar kasar Iran da kokarin kashe wutar rikicin ta hanyar Lumana. Shugaban Amirka Donald Trump ya bayyana gamsuwarsa da yadda ya ce kasashen duniya suka yi baki guda kan batun hana Iran mallakar makamin nukiliya.

Masu adawa da taron na G7 dai sun yi yinkurin yin tattaki har zuwa harabar taron na G7 a birnin Biarritz domin bayyana wa shugabannin kasashen rashin amincewarsu da duk wani mataki da za su dauka da sunan duniya baki daya. Sai dai tun ba su je ko ina ba 'yan sanda suka taka masu birki.