Matsayin taron G7 a kan Putin da Ukraine | Siyasa | DW | 05.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsayin taron G7 a kan Putin da Ukraine

Shugabannin kasashen da suka fi karfin tattalin arziki a duniya sun samu sabani a kan matakin ladabtar da shugaba Vladimir Putin na Rasha da ke ruruta rikicin Ukraine.

Daukacin shugannin kasashen G7 sun amince da ci gaba da matsa wa Vladimir Putin na Rasha lamba, da nufin tilasta masa tsame hannenya kwata-kwata daga rikicin da Ukraine ta ke fama da shi. Amma kuma sun ta dogon turanci dangane da matakin zahiri da ya kamata a dauka a kan shugaban na Rasha don ladabtar da shi. Wasu daga cikinsu irin su Amirka da Canada sun nemi a katse cinikin iskar gas da wasu kasashe na yammacin duniya ke yi da Rasha, lamarin da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ki amincewa da shi.

Amma dai shugabanninin kasashe bakwai da suka fi karfin tattalin arziki a duniya, sun yi barazanar sanya wa Rasha takunkumin karya tattalin arzikin ba, idan Putin ya yi kunnen uwar shegu da wannan bukatar da su mika masa. Sun yi kira gareshi da ya dauki matakan da suka wajaba don maido da zaman lafiya a gabashin kasar Ukraine.

Kana sun nemi Putin da ta ya gudanar da kyakyawar ma'amala da sabon shugaban Ukraine Petro Poroschenko. sannan kuma ya daina taimaka wa masu neman ballewa na gabashin Ukraine tare da kwashe duk kayan yaki da ya jibge a kan iyakar kasshen biyu. Idan ko ya ki yi to takunkumai za su iya shafar fannonin masana'antu da tsaro da kuma bankuna ne a Rashar.

Sakateren zartsawa na Kungiyar Gamayyar Turai, Jose Manuel Barosso ya nemi manyan kasashen duniya su taimaka wa Ukraine don ta samun damar tsayawa a kan kafafunta a fannin tattalin arziki da kuma siyasa. A watan Yuli mai zuwa ne dai EU ta ke da niyar gudanar da taron kwayen ukraine, da nufin samar da kudin da zai bayar wa kasar damar tayar da komadar tattalin arzikinta.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Zainab Mohammed Abubakar

Sauti da bidiyo akan labarin