Merkel: Za mu tabo batun cutar Ebola a taron G7 | Siyasa | DW | 06.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Merkel: Za mu tabo batun cutar Ebola a taron G7

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da ke daukar bakwancin taron G7 ta yi hira ta musamman da DW, inda ta ce za su fi mayar da hankali kan kasuwanci da tsaro da kiwon lafiya da ɗumamayar yanayi.

Shugabar gwamnatin ta Jamus ba ta yi wata-wata ba wajen nuna muhammincin raja'a a kan Rasha, wajen warware rikicin siyasa da ke addabar wasu sassa na duniya. Sai dai kuma wannan kasa ba ta da kgurbi a cikin jerin kasashen bakwai da ke da kujera a kungiyar G7. Angela Merkel ta ce ba za a rabu da Bukar ba a yakin basasa da ake fama da shi yanzu haka a Syriya, ba tare da gudunmawar gwamnatin Vladimir Putin ba. A cewarta ma dai, idan ba don gwamnatin Moscow ta tallafawa ba, da har yanzu ba a fara gano bakin zaren warware rikicin shirin nukuliyar Iran ba.

"Rasha na ci-gaba da zama a wani fannin abokiyar hulda mai muhimmaci. Mun hada kai da ita wajen neman warware rikicin kasar Ukraine, mun dama da ita a tattaunawar da kasashen nan shida masu karfin fada a ji a duniya ke yi da Iran a kan shirin nukiliya. Sannan kuma muna bukatar Rasha don neman warware rikicin kasar Syriya. Ina so in tuna muku cewar an yi nasarar kawar da makami masu guba a Syriya ne da gudunmawar Rasha."

Belgien Ebola Konferenz in Brüssel

Shugabar Laberiya za ta yi bayai kan Ebola a taron G7

Angela Merkel ta kuma yi korafi dangane da rashin daukan kwararan matakai domin kawar da cutar Ebola a lokacin da ta barke a yankin yammacin Afrika. Da ma dai a rana ta biyu ta taron na G7 shugabannin kasashen Afirka da dama ciki harda Muhammadu Buhari na tarayyar Najeriya za su halarci taron. Ita ma shugabar Laberiya Ellen Johnson Sirleaf da ke zama daya daga cikin kasashen da suka yi fama da cutar da Ebola mai saurin kisa ba za a barta a baya ba. Hasali ma dai a cewar Angela Merkel, batutuwan da suka shafi kiwon lafiya na sahun farko na ajendar taron na birnin Elmau.

"Lokacin da cutar Ebola ta barke, kasashen duniya ba su hanzarta kai dauki ba. Sun isa a makare, sannan kowa ya yi gaban kansa, lamarin da bai kamata mu sake gani ba. Ina ganin cewar halartar taron da shugabar Laberiya za ta yi, na tunatar mana da muhimmancin al'amuran kiwon lafiya."

Sai dai a lokacin da DW ta tabo matsalar tattalin arziki da kasar Girka ke fama da ita, shugabar gwamnatin Jamus ta nunar da cewar ko kadan wannan batu ba zai mamaye taron G7 ba. Ta na mai cewa za su yi waiwaye ne adon tafiya game da halin da tattalin arzikin kasashe bakwai da suka karfin masan'antu ke ciiki. Merkel ta ce idan dai a bangarenta Girka ta kasa shawo kan matsalar bashi da ke yi mata katutu, a fili ya ke cewa akwai wasu kasashen Turai da suka yi nasarar magance matsalar arziki da suka yi fama da ita.

Symbolbild zum Treffen Tsipras - Juncker in Brüssel

Firaministan Girka Tsipras na Kai ruwa da Eu kan bashi

"Za mu iya tabbatar da cewa Irland wacce ita ma ta yi fama da komabayan tattalin arziki ta yi nasarar murmurewa daga halin da ta samu kanta a ciki. Sannan kuma tattalin arzikin Portugal da kuma Spain na kan bunkasa. Sai kuma batun gammon bashin Girka. Amma ba nan ne gizo ke saka ba. Za mu yi nazarin inda aka kwana ne, sannan mu yi fatan ganin cewar tattaunawar da ake yi da Girka, haka ta cimma ruwa."

Shekaru takwas da suka gabata ne dai Jamus ta dauki bakwancin karshe na taron kasashen da suka fi karfin tattalin arziki a duniya na G8 a wancan lokaci kafin dakatar da Rasha daga cikin kungiyar.

Sauti da bidiyo akan labarin