Fargaba kan mamayar da Boko Haram ke yi a Borno | Siyasa | DW | 05.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Fargaba kan mamayar da Boko Haram ke yi a Borno

Al'ummar Najeriya na cigaba da nuna fargabarsu kan harin da kungiyar Boko Haram suka kai a garin Baga da kame hedikwatar rundunar kasa da kasa da ke yaki da ta'addanci.

Harin da aka kai a garin na Baga da ke kan iyakara Najeriya da kasar Chadi ya kasance mai daukar hankali jama'a saboda yadda aka afakawa sansanin sojojin kasa da kasa da Najeriyar da wasu kasashen makwabta irinsu Chadi da Kamaru da ma Jamhuriyar Niger suka kafa tare da fattatakar sojojin da ake sa ran su ne za su iya hada karfi su kai dauki ga duk wata barazana.

Wannan babban koma baya da sojojin suka samu ya sanya masu fashin baki kan harkokin tsaro a Najeriya irinsu Malam Kabiru Adamu cewar karbe yankin da ma kafa tutar da 'yan kungiyar ta Boko Haram suka yi abu ne mai tada hankali da hadari babba, inda ya kara da cewar "wannan yunkuri da su ‘yan Boko Haram suka yi alama ce da ke nuna cewa suna da tsari da bukatar da suke da ita, domin in ka duba ai garuruwan da suke kamewa na kan iyakar Najeriya ne da sauran kasashe wanda zai basu damar cin karen ba babbaka''.

Symbolbild zur Nachricht - Streitkräfte in Kamerun zerschlagen Boko-Haram-Schule

Harin garin Baga ya sanya sojin Najeriya tserewa daga sansanisu.

Tuni dai kungiyoyin kare hakin jama'a suka fara maida murtani a kan cigaba da kame garuruwan da ake yi, domin kuwa bayanai sun nuna cewa ya zuwa yanzu kanana hukumomi 14 ne ke karkashin ikon kungiyar ta Boko Haram a jihohin Borno da Yobe daidai lokacin da ya rage makonni 6 kafin a gudanar da babban zabe a kasar. To sai dai a daura da wannan, gwamnati na mai ikirarin cewa ta na iyakar kokarinta har ma da bayyana samun nasara kwato wasu garuruwan da aka kame a lokutan baya.

Yayin da gwamnatin ke wadannan kalamai, Auwal Musa Rafsanjani da ke zaman guda daga cikin 'yan kungiyoyin fararen hula a kasar ya ce akwai abin kunya ne fa abinda ke faruwa a fanin tsaron kasar, inda ya kara da cewar "wannan ya dada nuna mana cewa gwamnatin Najeriya na yin sakoci ko kuma an fi karfinta domin babu ta yadda za'a yi kana shugabanci a zo a kame wani bangare na kasarka amma kasa ido. Wannan babban abin kunya ne ga Najeriya".

Nigeria Anschlag 28.11.2014

Hare-haren Boko Haram a Najeriya sun yi sanadin hallaka mutane da dama.

Da dama dai na jinjina irin hadarin da irin mamayar da Boko Haram ke yi a Najeriya musamman ma sansani sojin da ke kula da sha'anin tsaro a yankin. Malam Kabiru Adamu kwararre a fanin tsaro a Najeriya ya ce "ba abu ba ne mai kyau a ce kusan sansani guda daya da ya rage a wannan yanki ya koma hannun 'yan bindiga. Ya kamata a ce su jami'an tsaron Najeriya sun shiryawa irin wannan harin, amma bisa ga bayanan da muka samu sojin Najeriya sun tsere har ma da mika makamansu ga abokan gabansu". Yanzu haka dai abinda al'ummar wannan yanki da ma kasar baki daya ke zuba idanu su gani shi ne irin martanin da gwamnatin kasar za ta maida kan wannan hari da irin matakan da za ta dauka wajen ganin ta maido da sansanin a hannunta kana da irin yunkurin da za ta yi wajen zabukan 2015 sun gudana a yankin.

Sauti da bidiyo akan labarin