Faransa za ta fice daga Mali a watan gobe | Labarai | DW | 06.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa za ta fice daga Mali a watan gobe

Kasar Faransa ta ce dakarunta da ke jagorantar fafutukar kawar da 'yan tawayen Mali da ke wasu sassan na arewacin kasar za su fice daga kasar cikin watan gobe.

default

a

Ministan harkokin tsaron Faransan Jean-Yves Le Drian ne ya shaida hakan inda ya kara da cewar Faransa ba ta da muradin kasancewa a kasar ta Mali na wani tsawon lokacin muddin dai al'amura su ka daidaita.

Wadannan kalamai na ministan tsaron na Faransa dai na zuwa ne daidai lokacin da kasashen duniya ke fafutukar tallafawa kasar ta Mali domin samun sukunin komawa yadda ta ke a baya.

Wannan ne ma ya sa kasar tarayyar Jamus ta ce za ta aike da sojinta arba'in wadanda su ka kware a fannin kiwon lafiya domin agazawa sojin na Mali kamar yadda ministan harkokin tsaron tarayyar Jamus din Thomas de Maiziere ya shaidawa jaridar Tagesspiegel wadda ake bugawa a nan tarayyar Jamus.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Muhammad Nasir Awal