1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa da Jamus na son ciyar da Turai gaba

Yusuf Bala Nayaya
September 7, 2018

Macron da Merkel na da buri na samun daidaito kan batutuwa da suka shafi 'yan gudun hijira da samar da sauyi kan huldodin Turai da wasu kasashe.

https://p.dw.com/p/34Uuj
Berlin Emmanuel Macron Antrittsbesuch Merkel
Hoto: picture-alliance/Sven Simon/A. Hilse

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za su tattauna kan tsare-tsaren 'yan gudun hijira da sauye-sauye kan harkokin kasashen da ke Turai da huldodin kasashen na Turai da wasu kasashe irinsu Siriya da Ukraine da kasashen yankin Balkans. Mai magana da yawun shugabar gwamnatin ta Jamus ya bayyana haka a wannan Juma'a.

Macron da Merkel na da buri na samun daidaito a tataunawarsu a birnin Marseille a kokarin da suke na ganin sun hada kai wajen ciyar da kasashen Turai gaba kamar yadda Steffen Seibert mai magana da yawun Merkel ya bayyana.