EU ta amince da shirin tallafi | Siyasa | DW | 21.07.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

EU ta amince da shirin tallafi

An kammala taron farfado da tattalin arzikin nahiyar Turai a Brussels inda shugabannin suka amince da Turai ta kashe Euro bilyan 750 wurin tallafa wa kasashen nahiyar murmurewa daga radadin coronavirus.

Belgien PK Abschluss EU-Gipfel

Emmanuel Macron shugaban Faransa tare da Angela Merkel shugabar gwamnatin Jamus

A cikin kusan shekaru 70 tarayyar Turai ba ta samu gagarumin tsari na ceton tattalin arzikin mambobin ta kamar nasarar da shugabannin nahiyar suka cimma. A yanzu sun amince su tara dubban miliyoyi na Euro domin kamfanoni da kananan masana'antun kasashe 27 da ke nahiyar su warware daga lahanin da coronavirus ta yi musu. Shugabar hukumar tarayayar ta Turai Ursula von der Leyen ta ce za a shimfida tsari da zai tabbatar da cewa dukkan kasashen nahiyar sun kashe kudin tallafin a bisa doka: ''Mun rubuta karara a cikin yarjejeniyar da muka cimma cewa kowa zai bi doka, kuma babu wanda zai yi gaban kansa, dole ne kowa sai ya bi dokoki da ka'idojin da muka shata wadanda ba su ci karo da tsarinmu na kudade ba. Babu shakka za mu fito da tsarin da zai tabbatar an yi amfani da kudin EU ta hanyar da ta dace.''

 

Kai ruwa rana da aka yi ta samu kafin a kai ga cimma matsaya daya tsakanin kasashen

Tun da farko kasashen da ke kudancin Turai irinsu Spain da Italiya da corona ta fi yi wa barna sun bukaci a ba su wani fifiko na musamman a wurin rabon wannan tallafi. To sai dai  kasashen Ostiriya da Holland da Sweden da kuma Finland sun bijire wa bukatar, abin da kuma ya tsawaita taron na EU. Sai dai a yanzu an daddale kuma har an yi wa Spain alkawarin samun tallafin Euro biliyan140. Abin da babu shakka ya sanya firaministan Spain Pedro Sánchez murna, inda ya yi bayani yana mai cewa: ''kasarmu ta yi kokari ta samu Euro bilyan 140 da za a ba mu a cikin shekaru shida. wadannan kudade sun kai kaso 11 cikin 100 na tattalin arzikin Spain na shekarar da ta gabata. A cikin wadannan kudade an ba mu milyan 72,700 a matsayin tallafi, amma sauran rance ne da za  mu biya daga baya.''

Tallafin na Euro bilyan 750 zai taimaka wajen magance matsalolin tattalin arziki da corona ta haifar a nahiyar

Shugabannin na Turai dai sun ce Euro bilyan 750 da aka ware na tallafin corona ga kasashen nahiyar na shekaru bakwai da yawansa ya kai tiriliyan 1.1 na Euro, za su taimaka wurin magance radadin da corona ta yi wa nahiyar. To sai dai duk da haka shugabar gwamantin Jamus Angela Merkel da ke jagorantar kasashen a jagorancin karba-karba ta ce akwai bangarorin da suke son bayar da fifiko a wurin kashe wadannan kudade: ''Mun sanya sharuda da ka'idojin amfani da wannan tallafi, da suka shafi yin sauye-sauye da kuma gyara domin gobe. Muna son a kashe kaso 30 na kudaden a bangaren alkinta muhalli da kuma fasahar zamani. Hukumar tarayar Turai za ta bi diddigin wannan amma kuma su kan su kasashe za su rinka duba wa suga ko ba su kaucewa hanya daga tsarin da muka amince da shi ba.''

Sai majalisar kungiyar tarrayar Turai ta tattuna kasafin ta kuma amince da shi kafin fara aiki da shi a matsayin doka

A yanzu tallafin ceton daga corona din na a matsayin kuduri ne har sai majalisar tarayyar ta Turai ta zauna ita kuma ta yi muhawara akai kafin ya zama doka . To amma koma dai mene ne masana tattalin arziki sun ce za a kai tsakiyar shekara mai zuwa kafin tattalin arzikin kasashen Turai din ya fara ganin tasirin wannan matsaya da shugabannin nahiyar suka cimma.

Sauti da bidiyo akan labarin