1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta fara mayar da 'yan kasarta China

May 30, 2020

Akalla 'yan kasar Jamus guda 400 sun fara komawa kasar China domin ci gaba da ayyukansu kamar yadda suka saba yi kafin bullar coronavirus.

https://p.dw.com/p/3d0gj
Deutschland Berlin | Wang Yi, Außenminister China & Angela Merkel, Bundeskanzlerin
Hoto: picture-alliance/Xinhua News Agency/W. Qing

Kamfanin jirgin sama na kasar Jamus Lufthansa ne ya fara wannan jigilar, wace ta kunshi Jamusawa da ke a aiki a matsayin manyan jami'ai a kamfanonin kasa da kasa da ke kasar ta China. Wannan dai shi ne karon farko da wata kasa a nahiyar Turai ke sake mayar da 'yan kasarta China tun bayan da aka kwashe su a lokacin da corona ta bunkasa a Chinar.

Hukumar bunkasa kasuwanci ta Jamus ce ta jagoranci wannan jigila, inda Jens Hildebrandt, babban darektan hukumar ke cewa, fara komawar Jamusawa kasar China wani babban ci gaba ne a kokarin da kasashen biyu ke yi na farfado da tattalin arzikinsu bayan da coronavirus ta dakatar da harkokin kasuwanci a tsakaninsu. 

Jamus dai na da kamfanoni sama da 5,200 da ke aiki a China, inda suke samar da ayyuka fiye da milyan daya a kasar.