Lufthansa shi ne kamfanin jirgin sama mafi girma a nahiyar Turai ta fuskar samun yawan fasinja da kuma yawan jiragen da kamfanin ke da su.
Kamfanin na da wasu kamfanonin jiragen sama karkashinsa wanda suka hada da German Wings da Swiss International Air Lines. Hedikwatar kamfanin na Lufthansa na birnin Kwalan da ke yammacin tarayyar Jamus.