1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Annobar Corona na ci gaba da yaduwa a sassan duniya

Ramatu Garba Baba
August 6, 2020

Indiya na daga cikin kasashen duniya da yawan wadanda suka kamu da cutar suka doshi miliyan 2 a yayin da kamfanoni ke kukan tafka asara a sakamakon annobar da ake fadin tashin ganin an dakile yaduwarta.

https://p.dw.com/p/3gUsG
Indien Bihar | Coronavirus | Gefahr für medizinisches Personal
Hoto: DW/M. Kumar

Yawan wadanda cutar sarkewar numfashi ta Coronavirus ta kama a kasar Indiya son doshi miliyan biyu, mutum sama da dari tara ta kama a kwana guda a yayin da ta riga ta kashe wasu kimanin dubu ashirin a cikin wata guda. Ma'aikatar Lafiya a kasar ta ce akwai wasu kusan dubu dari shida da ke jinyar cutar a yanzu haka.

Annobar na ci gaba da haifar da nakassu ga manya da kananan kamfanoni, katafaren kamfanin jiragen sama na Lufthansa,  ya sanar da yin asarar na Yuro biliyan daya da rabi a sakamakon takaita zirga-zirga a yayin da Kamfanin kera motoci na Toyota ya baiyana raguwar kusan dala biliyan bakwai a ribarsa, babu alamun al'amura za su iya sauya inda kamfanin ke hasashen tafka asarar a saboda annobar.


Kawo yanzu ba a kai ga samar da riga-kafin cutar ba a yayin da yawan wadanda cutar ta kama a duniya suka haura miliyan goma sha takwas tun bayan bullarta a kasar Chaina a Disambar bara.