Chadi ta yi barin wuta a Gamboru | Labarai | DW | 31.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Chadi ta yi barin wuta a Gamboru

Majiyoyin tsaro na kasashen Chadi da Kamaru sun nunar da cewa jiragen yakin dakarun kasar Chadi sun yi barin wuta a garin Gamboru da ke jihar Bornon Najeriya.

Garin na Gamboru dai na kan iyakar Najeriyar da Kamaru kuma dakarun sun yi barin wutar ne a kokarin da suke yi na fatattakar mayakan Boko Haram da suka addabi Najeriya da makwabtanta. Matsalar ta Boko Haram dai na shafar kasashe hudu kai tsaye da suka hadar da Najeriyar da Kamaru da Chadi da kuma Jamhuriyar Nijar da dukkaninsu ke da kan iyaka da Najeriyar. A wani labarain kuma rahotanni sun nunar da cewa akallah mayakan Boko Haram din 123 ne suka sheka barzahu yayin da dakarun kasar Chadi uku suka rasa rayukansu a wata fafatawa da 'yan Boko Haram din a Jamhuriyar Kamaru.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman