Bundestag ta amince da aikewa da jiragen saman sintiri a Afghanistan | Labarai | DW | 10.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bundestag ta amince da aikewa da jiragen saman sintiri a Afghanistan

Majalisar dokokin Jamus Bundestag ta amince da shawarar da majalisar ministocin ta yanke na tura jiragen saman sintiri samfurin Tornado guda 6 zuwa Afghanistan don taimakawa sojojin NATO su zakulo ´yan takifen Taliban musamman a kudancin kasar, inda ake fama da rigingimu. Wakilai 405 suka jefa kuri´ar amincewa da tura jiragen saman da kuma karin dakaru 500 yayin da wakilai 157 suka yi watsi da shirin. Yanzu haka dai Jamus na da sojoji dubu 3 a arewacin Afghanistan. ´Yan siyasar kasar da ke adawa da tura jiragen saman sun ce yin haka zai kara jefa dakarun Jamus cikin rikicin kasar.