Buhari na shirin tinkarar ′yan Boko Haram | Labarai | DW | 11.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Buhari na shirin tinkarar 'yan Boko Haram

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da kuma shugabannin kasashe makwabta za su gudanar da taron koli a birnin tarayya don daukan matakan yaki da Boko haram.

Shugaban Tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari zai dauki bakwancin taron koli da zai gudana a wannan Alhamis a birnin Abuja, domin tattaunawa tare da daukan matakan bai daya na yaki da kungiyar Boko Haram. Daukacin shugabannin kasashe hudu da ke makwabtaka da Najeriyar ne ake sa ran za su halarci wannan taro, ciki har da na Chadi da Nijar da kamaru da kuma Jamhuriyar Benin.

Tun dai bayan da ya yi rantsuwar kama aiki makwanin biyun da suka gabata ne, shugaba Muhammadu Buhari ya dukufa kan hanyoyin gano bakin zaren warware matsalar tsaro da ta addabin yankin Arewa maso gabashin Najeriya, inda ya ke bayar da karfi ga matakin hada guywa da kasashe makwabta don dakile Boko Haram.

Baya ga ziyarar da ya kai Jamhuriyar Nijar da kuma Chadi, Buhari ya halarci taron koli na kasashe bakwai da suka fi karfin masana'antu a duniya, domin neman goyon bayan kasa da kasa a fannin horon sojoji da kuma musayar bayanan sirri.

.